
Rahotanni sun bayyana cewa, Matatar man fetur ta Dangote ta rage farashin man fetur dinta daga 828 zuwa 699 watau an samu ragin har Naira 129 akan kowace lita kenan.
Rahotanni daga Petroleumprice.ng sun ce a ranar Juma’a ne matatar ta Dangote ta yi wannan ragin farashin.
Wani ma’aikacin matatar wanda baya so a fadi sunansa ya tabbatar da hakan ga jaridar Punchng.