Saturday, May 31
Shadow

Matsin Tattalin Arziki yayi yawa, ‘Yan Najeriya ba zasu iya biya ba>>Majalisar Tarayya tacewa Ministan sadarwa maza a dakatar da karin kudin kiran waya da ake shirin yi

Biyo bayan karin kudin kiran waya dana data da kamfanonin sadarwa suka yi, majalisar tarayya ta yunkuro dan dakatar da karin.

Hukumar sadarwa ta kasa, NCC tuni ta amincewa kamfanonin sadarwar su kara kaso 50 cikin 100 na kudin da suke caji.

Saidai kungiyoyin fafutuka da suka hada dana Kwadago, NLC da TUC sun ce basu amince da wannan kari ba.

‘Yan majalisar ta wakilai a ranar Talata sun baiwa ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani umarnin ya dakatar da kari kudin kiran wayar inda suka ce ‘yan Najeriya ba zasu iya biya ba musamman a wannan yanayi na matsin tattalin arziki.

Karanta Wannan  Addini Sauki Gareshi:Ko Tuntunbe ka yi zaka iya ajiye Azumi>>Inji Young Sheikh

Sai ranar Litinin me zuwa ne ya kamata a fara yin karin kudin kiran dana data, amma MTN a matsayin kamfanin sadarwa mafi girma a Najeriya Tun a wannan satin sun fara kara kudin kira.

A wata hira da jaridar Punchng ta yi da wakilin kamfanin, ya tabbatar da cewa sun fara kara kudin kira dana data amma a hankali zasu kammala karin akan duka abubuwan da suke sayarwa.

Abin jira a gani shine, Ministan sadarwa zai bi umarnin majalisar tarayya wajan dakatar da karin kudin kiran dana data kokuwa?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *