
Tsohon dan takarar shugaban kasa kuma jigo a jam’iyyar PDP, Gbenga Olawepo-Hashim ya zargi jam’iyyar PDP din da yunkurin taimakin Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya sake cin zabe.
Ya bayyana hakane bayan da jam’iyyar PDP tace dan kudu zata tsayar takarar shugaban kasa inda Gbenga yace hakan yunkuri ne na taimakawa Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya ci zabe a 2027.
Ya bayyana hakane a yayin hirar da aka yi dashi a Channels TV inda yace masu neman a tsayar da dan kudu takarar shugaban kasar irin wanda suka raba kafa ne a PDP suna cewa, suna tare da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu amma kuma suna cikin PDP.