Saturday, June 27
Shadow

Tun da na hau mulki cin hanci ya zama tarihi a Nijeriya – Tinubu

Tun da na hau mulki cin hanci ya zama tarihi a Nijeriya – Tinubu

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya tabbatar wa masu saka hannun jari na kasar Brazil cewa gyare-gyaren tattalin arzikin da ake aiwatarwa a Najeriya suna samar da ingantattun sakamako, inda ya yi ikirarin cewa “ba a sake samun cin hanci da rashawa ba” tun bayan da ya hau kujerar shugaban kasa.

Jaridar Tribune ta rawaito cewa Shugaban ya bayyana hakan ne a yayin wani taro da aka gudanar a ranar Litinin tare da ministoci daga kasashen biyu da kuma mambobin kungiyar kasuwanci ta Brazil, inda ya sake jaddada shirye-shiryen Najeriya na karfafa hadin gwiwa a bangaren fasahar zamani, samar da abinci, masana’antu da makamashi.

Karanta Wannan  Babu shugaban kasar da yana cikin hankalinsa zai jawoka jikinsa saboda yanda ka yi Alfahari da aika Tsohon shugaban kasa, 'Yar'adua Kabari, Shehu Sani ya gayawa El-Rufai

Tinubu ya bayyana tattalin arzikin Najeriya a matsayin “wata babbar kasuwa mai dimbin damammaki da kamfanonin Brazil ba su taba cin moriyarta ba.”

Ya amince cewa gyare-gyaren da ya fara aiwatarwa “sun kasance masu zafi a farko, amma a yau sakamakon yana bayyana.”

“A hankali jama’a suna fahimta. Muna da karin kudade a cikin tattalin arziki, kuma babu cin hanci da rashawa.”

Don nuna gaskiya da adalci, ya yi nuni da Babban Bankin Najeriya (CBN), inda ya ce: “Ba sai ka san wani ba kafin ka samu kudin waje da kake bukata. ‘Yan wasa da karairayi sun fita daga kasuwa. A kasuwar kudin mu, kofa a bude take ga dukkan kasuwanni.”

Karanta Wannan  Kalli Subhanallahi Ana ta yada Bidiyon kirkira na AI dake nuna wai shugaba Buhari yayi mummunan karshe, Saidai mutane nata Allah wadai da fadar cewa hukuncin bawa na ga mahaliccinsa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *