Tuesday, March 18
Shadow

Me magana da yawun shugaban kasa ya nemi a zartar da hukuncin ķķìsà kan matashiya ‘yar bautar kasa data soki Gwammatin Tinubu

Rahotanni sun bayyana cewa, me taimakawa shugaban kasa kan yada labarai, Temitope Ajayi ya nemi a zartar da hukuncin kisa kan matashiya Ushie Uguamaye saboda sukar da tawa shugaba Bola Ahmad Tinubu.

Kafar peoplesgazette ce ta wallafa cewa Temitope Ajayi ya nemi a yankewa Ushie hukuncin kisa saboda yace a zartar mata hukunci mafi tsanani da hukumar bautar kasa ta NYSC ta tanadar.

Saidai a bayaninsa, Ajayi, ya bayyana cewa, shi ba haka yake nufi ba, an canja masa manufar bayaninsa ne dan cimma wani buri.

Yace abinda yake nufi da zartarwa da Ushie hukunci mafi tsanani a dokar NYSC shine a koreta daga aikin bautar kasar, yace shi a iya saninsa wannan ne hukunci mafi tsanani a dokar NYSC ba hukuncin kisa ba.

Karanta Wannan  Mai Ɗaukar Hoton Da Ya Lashe Kambun Bajinta Na (Guinness World Record) Sa’idu Abdulrahman Ya Gana Da Captin Ahmed Musa

Lamarin Ushie ya dauki hankula sosai inda ciki hadda Atiku Abubakar, da Peter Obi da kungiyar kare hakkin bil’adama ta Amnesty international sun saka baki a ciki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *