Thursday, January 2
Shadow

Miji ya saki matarshi bayan da mawakin Amurka, Chris Brown ya sumbaceta

Wani magidanci a kasar Afrika ta kudu ya saki matarsa biyo bayan sumbatarta da mawakin kasar Amurka, Chris Brown yayi.

Mutumin me suna Lusaka dan kimanin shekaru 42 ya gamu da takaici ne bayan ganin hotunan sumbatar matarsa da Chris Brown din yayi.

Kwanannan dai Chris Brown din ya je kasar Afrika ta kudu inda yayi wasa sannan kuma ya gana da masoyansa inda a canne ya hadu da matar me shekaru 34.

Mijin yace abinda matar ta aikata rashin girmamashi ne kuma ya yiwa aurensu bacin da ba zai gyaru ba. Yace kuma abinda matar ta yi bai kamata ace matar aure ta aikata hakan ba.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyo: 'Yan Shi'a sun koka kan cirewa matansu hijabi da 'yansanda suka yi a Abuja

Mijin dai yawa matar magana dan ya mata fada amma sai ta gaya masa cewa, wannan ba wani abin tada hankali bane.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *