Friday, December 26
Shadow

Ministan ilimin Najeriya na so a faɗaɗa shirin NYSC zuwa shekara biyu

Ministan ilimi na Najeriya, Olatunji Alausa ya yi kira da a faɗaɗa shirin yi wa ƙasa hidima, NYSC daga shekara ɗaya zuwa shekara biyu.

Mista Alausa ya bayyana haka ne lokacin da ya kai wa babban daraktan hukumar, Birgediya Janar Olakunle Nafiu, ziyara a ofishinsa ranar Juma’a.

Haka kuma ministan ya buƙaci a faɗaɗa tare da inganta shirin koya wa masu yi wa ƙasa hidima sana’o’i.

Minista ya kuma yaba wa ayyukan hukumar NYSC, musamman wajen tantance tare da gano matasan da suka je sansanonin NYSC da takardun kammala karatu na bogi.

Ya kuma ce ma’aikatarsa za ta ci gaba da aiki tare da da hukumar wajen inganta harkokin ilimi a faɗin ƙasar.

Karanta Wannan  Ki kiyayi kanki ki janye zargin da kikewa dan mu in ba haka ba wallahi zamu durkusa mu gayawa Allah ya mana maganinki>>Matan Inyamurai dana Niger Delta suka gargadi Sanata Natasha Akpoti

Mista Alausa ya kuma yi kira da a riƙa tura masu yi wa ƙasa hidima domin koyarwa a makarantun ƙauyuka da karkara, domin cike giɓin malaman da ake da ƙarincin a irin waɗannan makarantu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *