
An gayyaci tsohon sanatan Kaduna ta Tsakiya, Sanata Shehu Sani ya shiga cikin Alkalan da zasu yanke hukunci kan wadda zata lashe gasar Sarauniyar kyau ta Najeriya amma yace baya so.
Tsohon sanata, Ben Bruce ne ya shirya wannan lamari wanda zai wakana a Otal din Federal Palace Hotel dake Legas.
Sannan ya gayyaci Sanata Shehu Sani ya zama cikin Alkalai.
Saidai a sanarwar da ya fitar ta shafinsa na sada zumunta, Sanata Shehu Sani yace baya son wannan gayyata kuma ba zai iya ba.
Yace matansa ba zasu ji dadi ba idan yayi wannan alkalanci saboda ko a tsakaninsu bai iya fitar da wadda ta fi wata kyau ba dan haka ba zai iya alkalanci akan matan da bai sani ba.
Saidai yace ya gode da wannan gayyata da aka masa.