Gwamnan Jihar Katsina, Dr. Umar Dikko Radda ya bayyana yanda wani shugaban kauye ya karbi Naira dubu dari bakwai ya amince aka kai hari akan kauyenshi wanda yayi sanadiyyar kisan mutane 30.
Gwamnan yace an samu hakanne a Guga dake Bakori.
Ya kara da cewa ba zasu kyale ko wanene aka samu da hannu a harkar ‘yan Bindigar ba.
Saboda rayuwar mutanen jihar tafi ta mutum daya ko wanene shi.