Monday, June 2
Shadow

Muguntar da El-Rufai yayi a baya ce take binsa saboda Alhaki kwikwiyo ne, Kuma ba zai yi nasara ba, saboda mutane da yawa basu yadda dashi ba saboda mayaudari ne kuma maciyin amanane>>Buba Galadima

Injiniya Buba Galadima ya bayyana cewa, Tsohon gwamnan Kaduna, Malan Nasiru Ahmad El-Rufai ba zai yi nasara ba a kokarin da yake na hada kan ‘yan jam’iyyar Adawa da kuma kalubalantar Gwamnatin Tinubu a zaben shekarar 2027.

Buba Galadima ya bayyana hakane a wata hira da jaridar Punchng ta yi dashi wadda shafin hutudole ya bibiya.

Yace El-Rufai ya saba ya shiga jam’iyya wadda me karfi ce tana kan hanyar Nasara shima ya samu Nasara.

Yace amma yanzu da yake kokarin farowa daga farko a yanzu ne zai gane wahalar da ake sha wajan gina jam’iyya da siyasa.

Yace amma matsalar El-Rufai itace bashi da alaka me kyau da mutane, ya taka mutane da yawa kuma mayaudari ne maci yin amanane dan haka babu wanda ya yadda dashi kuma dalili kenan da yasa ba zai yi nasara ba.

Karanta Wannan  Gwamnatin tarayya ta saka dokar ta baci a Onne saboda shigo da miyagun makamai Najeriya

Yace El-Rufai yayi maganganu na cin zarafi da batawa mutane da yawa rai, yace kai El-Rufai har Allah ya sabawa, yace dan haka babu wanda zai yadda El-Rufai ya jagoranceshi saboda maciyin amanane.

Yace Mahaukaci wanda bai san ciwon kansa ba wanda kuma bai san siyasa ba ko kuma wanene El-Rufai ba zai yadda ya bishi.

Yace El-Rufai ra’ayin kansa kawai yake bi da yaga ba zai samu abinda yake so ba zai yadda ku ya kama gabansa.

Yace yawa mutane da yawa Irin su Atiku, Obasanjo, Buhari da Tinubu. Yace dan haka mutumin dake da irin wannan tarihin duk wanda ya bishi lallai mahaukacine.

Karanta Wannan  Da Duminsa: Tinubu ya ba da umarnin sakin yaran da aka gurfanar a kotu kan zanga-zanga

Yace saidai idan masu bin El-Rufai din duk irinsa ne kuma Allah yana son hadasu guri daya ya halakasu.

Yace kai yama yi wuri ace an fara wannan hadaka, kamata yayi a Bar shugaba Tinubu ya mayar da hankali wajan mulkin Najeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *