Tuesday, March 17
Shadow

Mun baiwa ‘yan Najeriya Miliyan 24 tallafi>>Inji Gwamnatin tarayya

Gwamnatin tarayya ta sanar da baiwa ‘yan Najeriya miliyan 24 tallafi daban daban da suka hada dana bashi dana koya sana’a da dai sauransu.

Ministan kudi, Wale Edun ne ya bayyana haka a wata ganawa da manema labarai.

Ya kara da cewa tallafin da suka bayar sun hada da bangaren Noma, Makamashi, masana’antu kiwon lafiya da dai sauransu.

Hakan na zuwane a yayin da ‘yan Najeriya ke ta fama da kokawa da matsin tattalin arziki wanda yasa kayan masarufi suka yi tashin gwauron zabi.

Karanta Wannan  Daga Yau Na Yi Bankwana Da Goyon Bayan Kungiyar Kwallon Kafa Ta Manchester United, Saboda Na Samu Damar Mayar Da Hankali Kan Muhimman Abubuwan Da Suka Jibanci Rayuwata, Inji Zakari Haruna Ajiya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *