Wednesday, January 15
Shadow

Muna yin bakin ƙoƙarinmu kan matsalar tsaro – Gwamnatin Sokoto

Bayan an shafe kwanaki ana sukar yadda gwamnatin jihar Sokoto ke tafiyar da sha’anin tsaro, musamman bayan garkuwa da kuma kashe Sarkin Gobir na Gatawa, a yanzu hukumomin jihar sun bayyana cewa suna iyakar ƙoƙarinsu kan matsalar.

A makon da ya gabata ne ƴan bindiga suka kashe Sarkin Gobir, Muhammad Isa Bawa, bayan yin garkuwa da shi na sama da mako uku, lamarin da ya janyo wa hukumomi kakkausar suka.

Wasu dai a Najeriya na zargin hukumomi da gaza yin abin da ya kamata wajen kawar da matsalar tsaro a faɗin ƙasar.

Ƴan fashin daji na kai hare-hare a jihohin arewa maso yammacin ƙasar, yayin da har yanzu ake fuskantar hare-hare nan-da-can na ƙungiyar Boko Haram a yankin arewa maso gabas.

Karanta Wannan  Maiɗakin Tinubu ta musanta cewa za ta jagoranci yi wa ƙasa addu'a

Hukumomin Najeriya dai sun ce suna bakin ƙoƙarinsu wajen magance matsalar.

Sai dai kisan da aka yi wa sarkin na Gobir na Gatawa, Muhammad Isa Bawa ya nuna cewa har yanzu ƴan bindigar na ci gaba da gudanar da ayyukansu na kisa da ɓarnata dukiyar al’umma ba tare da tsoro ba.

Sokoto na cikin jihohin yankin na arewa maso yamma, waɗanda har yanzu waɗannan hare-hare ke ci gaba da wakana.

Amma a tattaunawarsa da BBC, kwamishinan harkokin cikin gida na jihar, Sharifu Abubakar Kamarawa ya ce gwamnati tana daukar dukkan matakan da suka wajaba wajen wanzar da tsaro a gabashin jihar inda aka yi garkuwa da Margayi Sarkin.

Karanta Wannan  'Yan Najeriya sun bayyana cewa man fetur din matatar man Dangote na dadewa kamin ya kare

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *