Mutumin da ya auri mata 3 a rana daya Arube Otor ya bayyana dalilinsa na yin hakan da kuma yanda zai gamsar dasu a gado.
A hirarsa da jaridar Punchng ya bayyana cewa mahaifinsa ma mata da yawa ya aura kuma a gida daya suka zauna ba zaka gane banbanci tsakaninsu ba.
Yace dan haka shima shiyasa yake son yayi gadon mahaifinsa.
Yace dama yana da mata daya kamin auren matan 3 kuma nan gaba yana sonya kara auren guda biyu.
Ya kara da cewa, game da maganar kwana, kowacce zata rika zuwa tana masa kwana 3 a turakarsa har kwanan kowacce ya zagayo.