Tsohon Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya bayyana cewa, ya samu karin lafiya sosai bayan da ya sauka daga kan mulkin Najeriya.
Shugaban ya bayyana hakane a wajan taron Jam’iyyar APC a jihar Katsina.
Yace duk da kokarin da yayi na gyaran kasarnan amma ya fuskanci suka daga mutane da yawa.
Yace wadanda basa kusa da Gwamnati basu san yanda ake gudanar da mulki da matsalar mulkin ba.
Yace bayan da ya sauka, mutane dake kai masa ziyara sun bayyana cewa, a yanzu yafi lafiya fiye da sanda yake kan mulki.
Buhari ya baiwa shuwagabanni shawarar su ji tsoron Allah.