Friday, January 23
Shadow

Na yi magana da Anthony Joshua da mahaifiyarsa, bayan Khàdàrìn da ya rutsa dashi>>Inji Shugaba Tinubu

Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa, Yayi magana da dan Damben Najeriya, Anthony Joshua da mahaifiyarsa.

Yace ya yiwa AJ gaisuwar abokansa 2 da suka rasu a hadarin sannan ya masa fatan samun sauki.

Shugaba Tinubu yace AJ yace masa yana samun kulawa me kyau.

Yace kuma yawa mahaifiyar AJ jaje inda tace tana godiya da kulawar da shugaban kasar ya nuna musu.

Karanta Wannan  Ba dan kìyàyyà ga wasu mutanene yasa aka yi yàkìn basasa ba>>Inji Tsohon Shugaban kasa, Yakubu Gowon

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *