Thursday, December 26
Shadow

Na yi mamakin sauke ni daga muƙamin minista – T Gwarzo

Tsohon ƙaramin ministan gidaje na Najeriya, Abdullahi Tijjani Gwarzo ya ce ya yi mamakin sauke shi da a aka yi daga muƙaminsa.

Yayin wata hira da BBC kwanaki bayan sauke shi , T Gwarzo ya ce babu wani laifi da ya yi, wanda ya janyo aka sauke shi daga muƙamin nasa, sabod a cewarsa ya yi iya baƙin ƙoƙarinsa a muƙamin da aka ba shi.

”Batun ya zo min da mamaki, domin ba na tunanin wani abu mai kama da wannan zai faru da ni”, in ji shi.

Ya ƙara da cewa Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya yi la’akari da tarayyarsu tun ta da can wajen naɗa shi muƙamin.

Karanta Wannan  Na yadda da shawarar daka bani cewa in rika tausayawa 'yan Najeriya>>Tinubu ya gayawa Atiku

Ya ce fiye da shekara 14 suna tare da Tinubu tun a jam’iyyar ACN, shi da Nuhu Ribadu da Sanata George Akuwam – da ke riƙe da muƙamin sakataren gwamnati a yanzu.

Sai dai ya ce Allah ne ke ba da mulki, kuma ya karɓe a duk lokacin da ya so, don haka ya ce yana gode wa shugaban ƙasar, bisa damar da ya ba shi a gwamnatin tasa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *