Friday, January 16
Shadow

Na yi ta kokarin a kara kudin man fetur amma Buhari yaki saboda tausayin talakawa>>Inji Tsohon Karamin Ministan Man fetur Ibe Kachikwu

Tsohon karamin ministan man fetur, Ibe Kachikwu ya bayyana cewa, babu yanda bai yi da tsohon shugaban kasa, Marigayi Muhammadu Buhari ba kan a kara kudin man fetur amma yaki.

Yace Buhari ya ki a kara kudin man fetur ne saboda tausayin talakawa da yake dashi.

Ya bayyana hakane a wata hira da aka yi dashi.

Kachikwu yace amma daga baya Buhari ya amince inda yace a fara maganar cire tallafin man fetur saidai Ministan yace Buharin yace masa idan hakan bai haifar da da me ido ba, zai sallameshi daga aiki.

Karanta Wannan  Najeriya zata fita daga talaucin da tae fama dashi>>Inji Shugaba Tinubu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *