Kudin Najeriya, Naira ta karye a yau inda aka sayi dala akan Naira 1,635.15 a farashin gwamnati a ranar Litinin.
Idan aka kwatanta da farashin Dalar a ranar Juma’a wanda aka siya a farashin Naira 1,631.21 za’a fahimci, Nairar ta fadi da farashin 3.9 kenan.
A kasuwar ‘yan Canji kuma farashin dalar ya kai 1,660.