Friday, December 26
Shadow

Najeriya ta ƙara kuɗin yin fasfo

Hukumar shige da fice ta Najeriya (NIS) ta sanar da ƙarin farashin yin fasafo wanda zai fara aiki daga ranar 1 ga Satumba, 2025, domin inganta inganci da tsaro a tsarin fasafo ɗin ƙasar.

A cewar hukumar, farashin fasafo na shekaru biyar mai shafi 32 wanda a baya yake kan naira 70,000 yanzu zai tashi zuwa naira 100,000, yayin da na shekaru 10 mai shafi 64 wanda a baya yake kan naira 120,000 zai koma naira 200,000.

Sai dai, farashin fasafo da ‘yan Najeriya ke yi a ƙasashen waje ba zai canza ba, inda za a ci gaba da biyan dala 150 kan fasafo na shekara 5 da dala 230 kan fasafo na shekara 10.

Karanta Wannan  Wani me laifi da aka yankewa hukuncin daurin rai da rai ya mùtù ya dawo yace a sakeshi ya gama zaman gidan yarin da yake tunda ya mùtù ya dawo

Hukumar ta bayyana cewa wannan sabon tsarin na nufin tabbatar da daidaito a ayyukan fasafo, tare da sauƙaƙa damar samun fasafo ga duk ‘yan Najeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *