Sunday, March 16
Shadow

Najeriya ta tabbatar da kashe sojojinta shida a Borno

Rundunar tsaron Najeriya ta tabbatar da harin da mayaƙan Boko Haram suka kai kan sojojinta a jihar Borno.

A wata sanarwa da kakakin hedkwatar tsaro ta Najeriya, Manjo Janar Edward Buba ya fitar, ya ce an kashe sojoji guda shida, sannan wani kwamandan ƴan sa-kai ya jikkata.

Sai dai Buba ya ƙara da cewa a gumurzun, sojojin sun samu nasarar kashe ƴan Boko Haram 34, sannan sun ƙwato wasu makamai.

Wannan ne karo na biyu a cikin wata biyu da mayaƙan Boko Haram suka kashe sojoji a Najeriya. A watan Nuwamban 2024, an kashe gomman sojoji a wasu hare-hare da mayaƙan suka kai kan sojoji a ƙauyen Kareto da ke ƙaramar hukumar Mobbar da ke jihar Borno.

Karanta Wannan  Kalli Hotunan yanda akawa wasu 'yan luwadi da aka kama bulala 80 kowannensu a kasar Indonesia

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *