
Rahotanni sun bayyana cewa, Najeriya ta tafka Asarar Naira Biliyan N824.66bn a shekarar 2024 a kasuwancin Danyen Man fetur.
Hakan ya bayyana ne a cikin rahotannin da ofishin kasafin kudi na tarayya ya fitar.
A shekarar 2023 gwamnatin tarayyar ta samu kudin shiga da suka kai Naira Tiriliyan N1.90tn saidai a shekarar 2024 kuma ta samu Naira Tiriliyan N1.08tn ne wanda hakan ke nuna an samu raguwar kaso 43.32 cikin 100 na kudin shigar daga kasuwancin Danyen man fetur.
Wannan bayanai na watanni 3 ne na karshen shekara bana gaba dayan shekarar ba.