
Najeriya ce ta zo matsayi na 6 a cikin kasashen da aka fi aikata ayyukan ta’addanci a Duniya a shekarar 2025.
A shekarun 2023 da 2024 Najeriya tana matsayi na 8 ne.
Kasar Burkina Faso ce ta zo a matsayi na farko sai kuma kasar Pakistan na biye mata baya inda kasar Syria ta zo ta 3.
Mali ce ta 4 sai kasar Nijar ta 5 sai Najeriya ta zo ta 6.
Hakanan rahoton yace an samu yawan mutanen da aka kashe ta sanadiyyar ta’addanci a Najeriya wanda yawansu ya kai mutane 565 jimulla.