
Hamshakin me kudin Duniya, Bill Gates ya bayyana cewa, nan da shekaru 20, watau 2045 zai Rabar da gaba dayan kudinsa.
Bill Gates ya bayyana hakane a shafin Gidauniyarsa ta Bill and Melinda Gates wadda suka kafa a shekarar 2000. Daga baya Wallen Buffet ya shiga tafiyar.
Ya bayyana hakane yayin bikin cikar gidauniyar shekaru 25 da kafuwa.
Hakanan a shekaru 25, Bill Gates ya bayar da Tallafin da ya kai na dalar Amurka Biliyan 100 kyauta.
Yace nan da shekaru 20 din zai nunka yawan kudin da yake bayarwa tallafi har sai kudin sa sun kare gaba daya, bai bayyana cewa zai barwa ‘ya’yansa ko sisi ba.
Bill Gates wanda shine me kamfanin Microsoft yace zaftare tallafin da kasashe masu kudi suka yi wanda a baya suke baiwa kasashe matalauta abin damuwa ne.
Yace baya so idan ya mutu a rika bayar da tarihin cewa ya mutu a matsayin me kudi.