Wednesday, January 15
Shadow

Nasan cewa matakan dana dauka a mulkina sun saka mutane wahala>>Shugaba Tinubu

Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa, yasan matakan da gwanatinsa ta dauka na tayar da komadar tattalin arziki sun kawo wahala.

Ya bayyana hakane a jawabin da yayi da safiyar yau na ranar Dimokradiyya.

Inda yace yana sane da wahalar da ‘yan kasa suke sha.

Ya bayyana cewa amma daukar matakan dolene dan dora Najeriya a turba me kyau wadda zata daina dogaro akan man fetur kadai dan samun kudin shiga.

Ya bayyana cewa wannan abu ne da ya kamata a yi shi da dadewa amma shuwagabannin da suka gabata ba su yi ba.

Karanta Wannan  Da Ɗuminsa: Ba Za Mu Tafi Yajin aiki ba – NLC ta bayyana

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *