NDLEA ta kama wata mata da ta ɓoye ƙwayoyi a cikin al’aurar ta.

An kama wata mata mai suna Ihensekhien Miracle Obehi da ta rufe kanta da hijabi don fitar da kwayoyi iri daban-daban zuwa kasar Iran ta hanyar boye su a cikin al’aurarta, cikinta da kuma jakarta.
Jami’an Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Ƙasa (NDLEA) su ka damke ta a filin jirgin sama na Port Harcourt, Jihar Rivers.
Obehi, wadda ta sanya hijabi don guje wa binciken tsaro, an cafke ta a zauren tashi na filin jirgin a ranar Lahadi, 3 ga Mayu, 2025, yayinda take ƙoƙarin hawa jirgin Qatar Airline zuwa Iran ta hanyar Doha, bayan samun bayanan sirri.
Bayan an bincike ta, an gano tanada kwayoyi guda uku da ta saka a al’aurarta, da wasu manyan kunsoshin kwayoyi guda biyu da aka ɓoye a cikin jakarta, sannan kuma ta hadiye kwayoyi 67 na hodar iblis, irin kwayar Class A.
Saboda haka, aka sanya ta a karkashin kulawa domin fitar da kwayoyin, inda ta fitar da dukkanin kunsoshin 67 bayan kwanaki.
Ta bayyana cewa an ce ta hadiye guda 70, amma bayan ta sha 67 ba ta iya ci gaba ba, sai ta saka guda ukun da suka rage a al’aurarta. Jimillar nauyin kwayoyin da aka samo daga jikinta ya kai kilo 2.523.