
Dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar AAC a zaben shakerar 2019 da 2023, Omoyele Sowore kuma mawallafin jaridar Sahara Reporters ya shiga gudun yada kanin wani da aka yi a Abuja.
Ya bayyana cewa shine zai kayar da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da sauran ‘yan takarar shugaban kasa a zaben 2027.
Yace ya kamata Gwammati ta baiwa bangaren wasannin motsa jiki muhimmanci inda yace suma zasu iya kawo kudaden shiga kamar yanda fetur ke kawowa kasarnan.