Tuesday, May 6
Shadow

Nijar ta ayyana Hausa a matsayin harshen da za’a rika amfani dashi a ƙasar

A Jamhuriyar Nijar gwamnatin kasar ta bayyana Hausa a matsayin harshen da za a rinka amfani da shi a kasar yayin da sauran harsuna ta ayyanasu a matsayin na magana.

Kazalika an kuma bayyana harshen Ingilishi da Faransanci a matsayin harsunan aiki.

To sai dai kuma ba dukkanin ‘yan kasar ne ke maraba da wannan mataki ba.

An kiyasta cewa akwai mutum miliyan 18 da ke jin harshen hausa a Jamhuriyar Nijar, abin da ake ganin wannan ne ya sanya gwamnatin kasar ta ayyana shi a matsayin harshen da za a rinka amfani da shi a kasar.

To sai dai kuma ba dukkanin ‘yan kasar ne wannan mataki ya yi wa dadi ba, inda wasu ke cewa ya kamata a yi nazari sosai a kai.

Karanta Wannan  Ban santa ba, Har Gaban Allah tazo ta yi karya, Fasto ya nesanta kansa da matar data ce addu'arsa tasa ta yi kudi amma daga baya aka ganta tana saida lemu

Harshen Hausa shi ne ke matsayin na uku a Afirka inda kasashe da dama a Afirka a ke samun masu jin harshen.

Akwai dai masu jin harshen Hausa a kasashe kamar Najeriya da Nijar da Kamaru da Ghana da Chadi da Sudan da Benin da Togo da Gabon da kuma Burkina Faso.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *