
Rahotanni sun bayyana cewa, mataimakin jakadan kasar Ingila a Najeriya, Simon Field ya kai wa dan Damben Najeriya, Anthony Joshua ziyara a Asibitin da ya ke kwance a jihar Ogun bayan Hadarin da ya rutsa dashi.
Sannan kuma ya gana da Gwamnonin Ogun, Dapo Abiodun dana Legas, Babajide Sonwo Olu kamar yanda me magana da yawun Gwamnan jihar Ogun,Kayode Akinmade ya bayyana.
Yace suna bibiyar lamarin.
A hukumance aka sanar da ofishin jakadancin kasar Ingila lamarin.
Hakanan sauran wanda suka yi hadarin da Anthony Joshua suma an sanar da ofishin jakadancin kasashensu abinda ya faru.