Ciwon zuciya wanda yayi tsanani yana bukatar kulawar kwararren likita, saidai idan bai yi tsanani ba, ana iya amfani da magungunan gargajiya wajan maganceta
Irin ciwon zuciyar da ake magancewa a gida shine wanda baya faruwa a kullun, watau na dan lokacine, sai kuma damuwa, da daurewar gabobi, sai da yawan gyatsa.
Wasu lokutan akwai wahala wajan gane ko banbance kalar ciwon zuciyar da ya kamata a magance a gida da wanda ya kamata aje Asibiti.
Idan aka ji wadannan alamu na kasa to a je Asibiti:
Ciwin kirji idan ya yi tsanani yana daurewa, yayi nauyi ko yana nusar mutum.
Idan mutum ya ji kamar zuciyarsa zata buga.
Idan aka ji alamar numfashi na neman daukewa.
Idan ba'a ji wadannan alamu na sama ba to za'a iya gwada maganin gargajiya na gida kamar haka:
Ana iya samun ts...