Bishiyar kwakwar manja:Surrukan dake tattare da Kwakwar manja ga lafiyar dan adam wajan rage hadarin kamuwa da cutar Daji da sauransu
Manja ya samo asali ne daga bishiyar kwakwa mai suna "oil palm trees ".
Yana Kunshe da sinadarai kamar haka :
- carotene
- antioxidants
- vitamin E.
Kwakwa dai kamar yadda aka sani wata diyar itace ce mai matukar amfani ga rayuwar bil'adama, kamar yadda masana a fannin kiwon lafiya suka bayyana. Kwakwa na daya daga cikin 'ya'yan itace mai matukar amfani, saboda da irin sinadarin da Allah Ubangiji ya zuba cikin ta.
Kwakwa na dauke da ruwa cikin ta kana har ila yau ana bare jikin kwakwa sannan a ci. Kwakwa ya rabu kashi biyu, akwai kwakwar manja kana akwai kwakwa wace bata dauke da manja. Dukkanin nau'oin kwakwa dai na dauke da sinadarai da suke da matukar amfani ga rayuwar bil'adama kamar yadda masana suka bayyana.
WANNAN SINADARAI NA MANJA SUNA INGANTA LAFIYA TAHANYOYI...