Tuesday, December 16
Shadow
Soja Boy ya yi magana game da wannan hoton shi da Rahama Saidu a daki

Soja Boy ya yi magana game da wannan hoton shi da Rahama Saidu a daki

Duk Labarai
Tauraron mawakin Gambara me yawan amfani da kalaman batsa, wanda aka fi sani da Soja yayi martani bayan ganin wani hotonsa shi da Rahama Saidu a kan gado Hoton dai na AI wanda yayi ta yawo a kafafen sadarwa. Abin ya bashi dariya inda yace amma yanayin dakin ya burgeshi. Hakan na zuwane bayan da aka ga hotuna inda Soja Boy ya rungumi Rahama da kuma inda ya gaisa da ita.
Kalli Bidiyon: Mawaki 442 ya musuluntar da baturiyar da yakw waka da ita bayan da halayensa suka burgeta

Kalli Bidiyon: Mawaki 442 ya musuluntar da baturiyar da yakw waka da ita bayan da halayensa suka burgeta

Duk Labarai
Tauraron mawakin Gambara, 442 ya bayyana cewa baturiyar da aka ga suna waka tare da ita, ta karbi addinin Musulunci. Yace tana ganin yanda yake zuwa yana Sallah shine abin ya burgeta ta nuna masa sha'awar shiga Musulunci. Yace zai koyar da ita yanda zata bautawa Allah. https://www.tiktok.com/@mr442_/video/7550381377196150034?_t=ZS-8zmituSwmhd&_r=1
Ana ta surutu wai muna hada maza da mata a wajan Maulidi, to ba zamu daina hada maza da mata a wajan maulidi ba>>Inji Anisee

Ana ta surutu wai muna hada maza da mata a wajan Maulidi, to ba zamu daina hada maza da mata a wajan maulidi ba>>Inji Anisee

Duk Labarai
Shahararren dan darika, Masoyin Shehu Tijjani Alhaji Anisee ya bayyana cewa, ba zasu daina hada maza da mata a wajan Maulidi ba Ya bayyana hakane a matsayin raddi ga wani malamin darika da yace saboda hada maza da mata a wajan Maulidi ya kamata a daina yinsa. Saidai Anisee yace a ko inama ana hada maza da mata dan haka su ma a wajan Maulidi ba zasu daina ba.
Faduwar Farashin Abinci: Baku ga komai ba, nan gaba farashin zai kara faduwa sosai kuma gidan kowa sai ya wadata>>Iniji Gwamnatin Tinubu

Faduwar Farashin Abinci: Baku ga komai ba, nan gaba farashin zai kara faduwa sosai kuma gidan kowa sai ya wadata>>Iniji Gwamnatin Tinubu

Duk Labarai
Gwamnatin Tarayya tace 'yan Najeriya basu ga komai ba game da faduwar farashin Abinci da aa gani. Hakan na zuwa ne bayan da hukumar kididdiga ta NBS ta tabbatar da cewa, farashin kayan masarufi yayi ksa a Najeriya inda a yanzu makin bai wuce 20 ba. A yayin hira da manema labarai, me baiwa shugaban kasa shawara akan tattalin arziki, Tope Fasua yace abincin zai sake karyewa sai ya koma kasa da maki 10. Hakan na zuwane yayin da manoma a Arewa ke kokawa da cewa, sune ake hari wannan karya farashin abincin da ake.
Kalli Bidiyo: Akwai wadanda suka fini kudi a Najeriya>>Inji Dangote

Kalli Bidiyo: Akwai wadanda suka fini kudi a Najeriya>>Inji Dangote

Duk Labarai
Attajirin Najeriya, Aliko Dangote ya bayyana cewa akwai wanda suka fishi tsabar kudi a Nijeriya. Yace amma basu saka kansu cikin irin rigimar da ya saka kanshi ba. Yana magana ne kan gina matatar man fetur dinsa da kuma rikicin da ya kunno kai tsakaninsa da kungiyar NUPENG. Dangote yace amma dole ne sai an tallafawa gwamnati, yace ba komai ne za'a nade hannu ace wai gwamnati ce zata yi ba. Yace akwai abubuwan da dole sai mutane masu zaman kansu sun saka hannu, yace amma irin abinda ake masa zai sa mutane su guji zuwa zuba hannun jari a Najeriya. https://twitter.com/Imranmuhdz/status/1967987170138079720?t=jK8EwhBa8X1in8Zo76GyHQ&s=19
Yayinnda manoma ke Korafi: Farashin kayan abinci ya sade faduwa kasa

Yayinnda manoma ke Korafi: Farashin kayan abinci ya sade faduwa kasa

Duk Labarai
Hukumar ƙididdiga ta Naajeriya, NBS, ta ce farashin kayayyaki ya faɗo karo na biyar a jere a ƙasar, a watan Agusta 2025, lamarin da ya kawo sauƙi ga mutanen ƙasar. Alƙaluman da hukumar ta fitar sun nuna cewa, farashi ya sauko daga 21.88 a watan Yuli zuwa 20.12 a watan Agustan 2025. Abin da ke nuna cewa an samu raguwar kashi 1.76 cikin ɗari daga watan na Yuli zuwa Agusta. Hakan kuma na nufin farashin ya rikito idan aka kwatanta da 32.15 ciki ɗari da aka samu a watan Agustan 2024. Sai dai alƙaluman ba su yi wani tasiri na azo-a-gani ba a yankunan karkara, inda kuɗin mota da rarraba kayayyaki ke ci gaba da janyo tsadar kayayyaki fiye da a birane. Sai dai abinci, wanda shi ne ja gaba wurin kayayyakin da farashinsu ke ƙaruwa ya dawo matsakaici a watan na Agusta a ƙasar, ko da yake y...
Albashin da nake biyan Direbobin Tankana ya fi na wanda ya kammala jami’a>>Inji Dangote

Albashin da nake biyan Direbobin Tankana ya fi na wanda ya kammala jami’a>>Inji Dangote

Duk Labarai
Attajirin Najeriya, Aliko Dangote ya bayyana cewa, Albashin da yake biyan direbobin Tankarsa ya fi na wanda ya kammala jami'a. Dangote ya bayyana hakane a wata ganawa da yayi da manema labarai inda yayi karin haske kan rikicinsa da Kungiyar NUPENG. Ya kuma gayyaci direbobin NUPENG duk wanda bai da aiki ya je zai bashi aikin tukin. Dangote yace Albashin Direban tankarsa ya nunka mafi karancin Albashin sau 4 wanda akalla zai kai sama da Naira dubu dari uku kenan.