Ministan yaƙin Isra’ila ya sauka daga muƙaminsa
Ministan yaƙi na Isra'ila, Benny Gantz ya fice daga cikin gwamnatin Netanyahu.
Yayin da yake jawabi a wani taron manema labarai, Mista Gantz ya ce firaministan ƙasar Benjamin Netanyahu ya ƙi bari a samu abin da ya kira 'tabbatacciyar nasara' kan Hamas.
Ministan ya ƙara da cewa dole ne Mista Netanyahu ya sanya ranar da za a gudanar da zaɓukan ƙasar.
Tun a ranar Asabar mista Gantz ya yi niyyar gabatar da jawabin nasa, to amma sai ya jinkirta saboda kuɓutar da wasu Isra'ilawa da sojojin ƙasar suka yi a Gaza.
Ficewar jam'iyyarsa daga gwamnatin, ba zai kawo ƙarshen gwamnatin ba, to amma zai ƙara matsin lamba kan mista Netanyahu kan sukar da yake sha a ciki da wajen Isra'ila.
Dama dai tun cikin watan Mayun da ya gabata, Benny Gantz ya yi barazanar yin murabus daga majalisar yaƙin ...