Maniyyata 737 sun tashi daga Najeriya ranar Litinin duk da yajin aiki
Maniyyata Hajjin bana daga Najeriya na ci gaba da tashi zuwa ƙasa mai tsarki duk da yajin aikin 'yan ƙwadago da ya haddasa tsaiko a filayen jirgin ƙasar.
Hukumar Alhazai ta Ƙasa National Hajj Commission of Nigeria (Nahcon) ta ce aƙalla maniyyata 737 ne suka tashi a yau Litinin daga jihohin Kwara da Sokoto.
Nahcon ta ce jirgin Air Peace ne ya fara tashi a yau daga birnin Ilorin na jihar Kwara da mutum 311 da misalin ƙarfe 9:52 na safe.
Sai kuma wani jirgin Flynas da ya sake tashi da mutum 426 daga jihar Sokoto.
Alƙaluman da hukumar ta wallafa sun nuna cewa zuwa yanzu jimillar maniyyata 38,249 aka kwashe zuwa Saudiyya don gudanar da babbar ibadar ta addinin Musulunci.