Hukumar Hisbah A Jihar Kano Ta Cafke Shahararren Dan TikTok Mai Rawa Da Mata Lawancy.
A ci gaba da sumamen tsaftace kafafen sada zumunta da Hukumar Hisbah ta jihar Kano ke yi, ta cafke matashin nan Rabi'u Sulaiman da aka fi sani da Lawancy.
Hisbah na zarginsa da ci gaba da raye-rayen baɗala da riƙe hannun mata a bidiyo.
Idan za ku iya tunawa ko a shekarar 2023 ma Hisbah ta taɓa kama shi, amma ya nemi afuwa ya ce ya tuba.
Rahoton da muke samu na cewa, Kungiyar Kwadago ta NLC zata ci gaba da yajin aikin da ta dauri aniya gobe, Litinin bayan zaman sulhu da gwamnati ya ci tura.
A yau lahadi ne dai aka zauna tsakanin wakilan gwamnatin tarayya daga majalisar tarayya da kungiyoyin kwadago na NLC da TUC dan cimma matsaya kan mafi karancin Albashi, saidai an kare zaman ba tare da cimma matsaya ba.
Da misalin karfe 5:50 PM ne dai aka fara zaman inda aka kareshi da misalin karfe 8:45 PM.
Kakakin majalisar dattijai, Godswill Akpabio bayan taron, ya gayawa manema labarai cewa gwamnati ta roki kungiyoyin kwadagon kan su janye yajin aikin nasu amma suka kiya.
Akpabio yace idan aka yi yajin aiki, abubuwa da yawa hadda asibitoci a kasarnan zasu tsaya cik.
Duk da haka dai ya sake rokon kungiyoyin kwadagon da ...
Rahotanni sun bayyana cewa, shugaban Israela, Benjamin Netanyahu ya amince da tsagaita wuta akan Falas-dinawa bayan tursasawar kasar Amurka.
Rahoton yace, Israela ta amince da tsagaita wutarne a Yau, Lahadi.
A ranar Juma'ar data gabata ne dai Shugaba Biden ya gabatar da tsarin na tsagaita wuta wanda Benjamin Netanyahu yayi watsi dashi.
Saidai a yau ya amince.
Hakanan akwai rahotannin dake cewa, itama kungiyar Hamas ta amince da tsarin, amma bata sanar da hakan a hukumance ba.
Me baiwa Benjamin Netanyahu shawara kan harkokin kasashen waje, Ophir Falk ne ya bayyana hakan inda yace ba shiri bane me kyau amma suna son kubutar da duka mutane su dake hannun Hamas shiyasa suka amince dashi.
Saidai ya nanata aniyarsu ta son ganin bayan kungiyar ta Hamas.
Tauraron Mawakin Hausa, Nazir Ahmad Sarkin Waka ya saka hotunan 'ya'yansa da suka yi wasa da hoda.
Nazir ya saka su a shafinsa na sada zumunta inda yace sun ce masa sun shafa Hoda, shi kuma yace musu Toh.
Bidiyon batsa na wani Fasto Lucian dan kasar Uganda ya bayyana.
Bidiyon ya bayyana faston yana lalata da matar wadda ba'a san ko wacece ba sannan yana daukar bidiyon da kansa.
Faston dai yayi suna sosai a kasarsa ta Uganda saboda warkewa da yayi daga cutar Ebola.
Saidai tuni ya fito ya karyata cewa bashi bane a cikin bidiyon.
Saidai wadanda suka sanshi sunce lallai shine a Bidiyon.
Tauraruwar Fina-finan Hausa, Hadiza Gabon kenan a wadannan hotunan wanda aka dauka daga wajan bikin zagayowar ranar Haihuwarta da ta yi jiya.
Hadiza ta yi bikin zagayowar ranar haihuwarta inda ta cika shekara 35 da haihuwa.
Gwmanatin Najeriya ta ce za ta ci gaba da bai wa ma'aikatan ƙasar ƙarin albashin wucin gadi - da ta fara biya wata shida ta suka gabata - har zuwa lokacin da za a kammala cimma matsaya kan mafi ƙarancin albashi a ƙasar.
Cikin wani jawabi da ya yi wa manema labarai ranar Asabar a Abuja, ministan yaɗa labaran ƙasar, Mohammed Idris ya ce wa'adin mafi ƙarancin albashi da aka yi a shekarar 2019 ya ƙare ne ranar, 8 ga watan Afrilun 2024.
Sai dai ministan bai bayyana adadin kuɗin da gwamnatin ke biya a matsayin albashin wucin gadin ba, to a baya gwamnatin ta ce za ta riƙa biyan ma'aikatan ƙarin naira 35,000 a kan albashinsu kowane wata har na tsawon wata shida.
A ranar juma'a ne dai ƙungiyoyin ƙwadogon ƙasar suka ce za su tsunduma yajin aiki daga gobe Litinin, kasancewar wa'adin ranar 31...
Wasu Ministocin Isra’ila biyu masu tsatsauran ra’ayi sun yi barazanar ficewa daga gwamnatin hadin gwiwar ƙasar idan har Benjamin Netanyahu ya amince da tayin sabuwar yarjejeniyar zaman lafiya da shugaba Biden na Amurka ya gabatar.
Yarjejeniyar da Mista Biden ya sanar ta samu karɓuwa daga ɓangaren ƴan adawa a Isra’ila da ƙasashe masu shiga tsakani.
A ranar juma'a ne shugaba Biden ya yi tayin tsagaiwa wutar ta hanyar bullo da matakai uku, da suka haɗa da tsagaita wuta na mako shida a matakin farko.
Tare da janyewar dakarun Isra'ila daga wurare masu yawan jama'a a Gaza.
Sannan ya ce yarjejeniya za ta bayar da damar sakin Isra'ilawan da Hamas ke garkuwa da su da kuma tsagaita wuta na dindin tare da sake gina Gaza.
To sai dai ministan tsaron Isra'ila Itamar Ben-Gvir, ya ce duk wa...