NDLEA ta kama muggan ƙwayoyi na naira biliyan 2.1 a Legas da Fatakwal
Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun ƙwayoyi ta Najeriya, NDLEA ta ce jami'anta sun samu nasarar kama muggan ƙwayoyin da kuɗinsu ya kai kimanin naira biliyan 2.1 a biranen Legas da Fatakwal
Cikin sanarwar nasarar mako-mako da hukumar ke fitarwa ta ce a ranar Juma'a 31 ga watan Mayu, jami'anta tare da haɗin gwiwar sauran jami'an tsaro a filin jirgin sama na Murtala Mohammed da ke Legas suka kama wasu manyan jakankuna maƙare ƙulli 320 na tabar wiwi da nauyinta ya kai kilogiram 164.50 da aka yi safararta daga Canada.
Hukumar ta ce ta kama mutumin da take zargi da safarar tabar - da aka yi ƙiyasin kuɗinta ya kai naira miliyan 960, - mai suna an kama Ughenu Nnaife Francis, wanda ya shaida wa jami'an hukumar cewa naira miliyan shida aka biya shi domin shigar da kayan Najeriya.
NDLEA ta ...