Karanta Cikakken bayani kan Rayuwar AM. Yerima, Shekararsa Nawa, Dan wace jihane, kuma waye mahaifinsa na gaskiya?
Tun bayan da aka samu wata hatsaniya a ranar Talata da yamma 11 ga watan nan na Nuwamba 2025, a tsakanin ministan babban birnin Najeriya, Abuja, Nyesom Wike da jami'an sojin ƙasar saboda sojojin sun hana ministan shiga wani fili, ake ta yaɗa labarai da ra'ayoyi daban-daban a kan lamarin.
Baya ga fassara da ake yi wa lamarin ta ɓangarori daban-daban - na siyasa da mulki da kuma dokoki da ƙa'idoji na mulki, wani abu kuma da ke ɗaukan hankalin jama'a shi ne, jagoran sojojin da suka yi wannan dambarwa da ministan na Abuja da tawagarsa.
Jagoran tawagar sojojin shi ne Laftanar AM Yerima, wanda matashin ƙaramin hafsan sojin ruwa na Najeriya ne, wanda kuma ya kasance ne a wajen bisa umarnin mai gidansa tsohon shugaban rundunar sojin ruwa ta Najeriya, Vice Admiral Awwal Zubairu Gambo (mai rit...








