Hoto: Dansanda ya kash-she wannan matashin saboda yaki bashi cin hancin Naira 200
Ana zargin 'yansanda sun kashe wannan mutumin me shekaru 40 a titin Azikoro Road dake Yenagoa ta jihar Bayelsa saboda yaki bada cin hancin Naira dari biyu(200).
Rahoto ya bayyana cewa, mutumin me suna Benalayefa Asiayei yana kan hanyarsa ta komawa gidane daga wajan aiki da misalin karfe 8 na yamma yayin da aka kasheshi.
Bayan da 'yansandan suka kasheshi, sun tsere daga wajan amma wani daga cikin shaidun abinda ya faru sun dauki hotunansu.
Kakakin 'yansandan jihar, Musa Mohammed ya tabbatar da faruwar lamarin kuma yace sun tantance wanda ake zargi.
Iyalan mamakin sun ce suna neman adalci.