Tuesday, December 24
Shadow
Kuma Dai:EFCC ta sake kama wani matashi saboda lika Kudin Naira a wajan biki a jihar Gombe

Kuma Dai:EFCC ta sake kama wani matashi saboda lika Kudin Naira a wajan biki a jihar Gombe

Gombe
Hukumar yaki da rashawa da cin hanci ta EFCC ta sake kama wani matashi a jihar Gombe me suna Zachariyya Muhammad saboda yin likin kudin Naira a wajan wani biki. An kama shine ranar Asabar, 24 ga watan Mayu bayan ya lika kudin Naira dari 200 a wajan wani bikin G-Connect. Ko da aka nuna masa bidiyonsa yana likin, ya amsa cewa lallai shine, hukumar zata gurfanar dashi a gaban kotu. A baya dai EFCC ta kama mutane da yawa a jihar Gombe shima.
Hoton Sojan Najeriya da aka kama ya saci harsasai

Hoton Sojan Najeriya da aka kama ya saci harsasai

Tsaro
Hukumomin soji dana CJTF a jihar Borno sun kama wani soja da laifin satar harsasai. An kama sojan ne me suna Corporal Francis Bako a tashar motar Kano dake Maiduguri. An kamashi ne bayan samun bayanan sirri akan satar harsasan da yayi. Sojan dai na kan hanyar zuwa Kadunane bayan da aka kamashi da harsasan guda 602 kuma yana tsare yanzu haka.
Matar aure ta dirkawa mijinta harsashi ya mutu har lahira bayan data kamashi yana cin amanarta da makwabciyarsu yayin da yake shirin tserewa

Matar aure ta dirkawa mijinta harsashi ya mutu har lahira bayan data kamashi yana cin amanarta da makwabciyarsu yayin da yake shirin tserewa

Auratayya
18665874 - a closeup of the lock of a jail cell with iron bars and a bunch of key in the locking mechanism with the door open Wata mata me shekaru 33 a kasar Afrika ta kudu ta dirkawa mijinta harsashi ya mutu har lahira bayan data kamashi yana lalata da wata. Tuni dai hukumomi suka kama matar bisa zargin kisan kai. Suna zaune gida dayane dai da matar da mijin yayi lalata da ita. Kuma da matar tasa ta fuskanceshi da maganar, sai yayi yunkurin tserewa, saidai ta yi amfani da bindigarsa ta harbeshi ya mutu. Kakakin 'yansanda na yankin Limpopo, Col Malesela Ledwaba ya tabbatar da faruwar lamarin inda yace auna bincike.
Karanta Jadawalin yawan likitocin da kowace jiha ke dasu a fadin Najeriya

Karanta Jadawalin yawan likitocin da kowace jiha ke dasu a fadin Najeriya

Kiwon Lafiya
Wannan jadawalin yawan likitocin da kowace jiha ke dasu ne a Fadin Najeriya: Lagos: 7,385 FCT: 4,453 Rivers: 2,194 Enugu: 2,070 Oyo: 1,996 Edo: 1,777 Kaduna: 1,524 Anambra: 1,518 Ogun: 1,511 Kano: 1,477 Delta: 1,456 Osun: 1,294 Plateau: 1,200 Imo: 1,110 Kwara: 1,016 Ebonyi: 899 Akwa Ibom: 888 Abia: 829 Cross River: 826 Ondo: 743 Borno: 736 Bayelsa: 727 Ekiti: 695 Benue: 621 Sokoto: 602 Katsina: 562 Nassarawa: 552 Niger: 494 Gombe: 485 Bauchi: 443 Kogi: 418 Adamawa: 280 Yobe: 275 Kebbi: 273 Zamfara: 267 Jigawa: 255 Taraba: 201
Da Duminsa: Kungiyar kasashen Turai tace a kakabawa Israela takunkumi saboda kisan kiyashin da takewa Falas-dinawa

Da Duminsa: Kungiyar kasashen Turai tace a kakabawa Israela takunkumi saboda kisan kiyashin da takewa Falas-dinawa

Labaran Falasdinawa, Labarin Yakin Gaza, Yakin gaza da isra'ila
A karshe dai, kasashen Tarayyar Turai karkashin EU sun juyawa kasar Israela baya. Kasashen sun fito sun nemi a kakabawa kasar Israela takunkumi saboda kisan kiyashin da takewa Falas-dinawa. Hakan ya biyo bayan nacewa da kasar ta yi cewa sai ta shiga Rafah inda dubban fararen hula na Falasdinawa ke gudun Hijira. Kasar kuma ta kai wani mummunan hari a sansanin 'yan gudun hijirar wanda ya kone mutane akalla 50 kurmus ciki hadda yara kanana. Lamarin ya jawowa kasar Israela Allah wadai wanda daga baya Firaministan kasar, Benjamin Netanyahu ya fito yace kuskurene kuma suna bincike akai.
Ji abinda sarki Aminu Ado Bayero yayi bayan da kotu tace ya daina kiran kansa Sarkin Kano

Ji abinda sarki Aminu Ado Bayero yayi bayan da kotu tace ya daina kiran kansa Sarkin Kano

Kano
A jiya, Talata dai an samu hukunce-hukuncen kotu biyu masu karo da juna wanda daya na babbar kotun tarayya ce dake Kano data ce a sauke Sarki Muhammad Sanusi II saga sarautar Kano. Mai shari'a, S. Amobeda ne ya bayyana hakan a hukuncin daya fitar inda yace a mayar da Aminu Ado Bayero a matsayin sarkin Kano. Saidai itama babbar kotun Kano karkashin mai shari', Amina Aliyu tace Sarki Muhammad Sanusi II ne sarkin Kano inda kuma tace Sarki Aminu Ado Bayero ya daina bayyana kansa a matsayin sarkin Kano. Saidai duk da wannan hukunci, Sarki Aminu ya ci gaba da zama a karamar fadar dake Nasarawa inda yace ci gaba da ayyana kansa a matsayin sarkin Kano. Rahotanni sunce har yanzu akwai jami'an tsaro da aka girke a gidan Nasarawa wanda kuma suna hana ma mutane bin hanyar sai wanda ya zama...
Sarki Aminu Ado Bayero ne zabina>>Inji Tauraruwar Fina-finan Hausa, Sadiya Kabala

Sarki Aminu Ado Bayero ne zabina>>Inji Tauraruwar Fina-finan Hausa, Sadiya Kabala

Kannywood, Sadiya Kabala
Tauraruwar Fina-finan Hausa, Sadiya Kabala ta bayyana cewa, Sarki Aminu Ado Bayero e zabinta. Ta bayyana hakane ta shafinta na sada zumunta i da tace bata hana kowa ya bayyana zabinsa ba. Sadiya ta saka hoton sarkin tana waka akai. Rikicin sarautar Kano wadda ya taso bayan da majalisar jihar ta sauke Sarki Aminu Ado Bayero ta mayar da tsohon Sarki Muhammad Sanusi II akan karagar sarautar ya raba kawunan mutane da yawa a ciki da wajen jihar ta kano.