Labari Me Dadi:Zamu rabawa mutane Miliyan 75 kudade kyauta, tsarin Npower ya dawo>>Inji Gwamnatin Tinubu
Gwamnatin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ta bayyana dawo da tsarin tallafawa mutane wanda ta tsayar a watannin da suka gabata.
Ministan kudi, Wale Edun ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ga manema labarai a matsayin shiri na cika shekara daya da gwamnatin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ta yi.
Tsarin dai wanda ya hada da ciyar da dalibai, da Npower, da baiwa mutane gajiyayyu kudin tallafi da tallafawa 'yan kasuwa da sauransu a yanzu ya dawo zai ci gaba da aiki.
Ministan yace dama a baya an tsayar da tsare-tsarenne dan bincike da kuma kawar da matsalolin dake cikin tsarin kuma yanzu an kammala.
A dambarwar da aka yi ta dakatar da tsarin, ta hada da dakatar da ministan jin kai Beta Edu wadda aka yi zargin ta aikata ba daidai ba.
Saidai a yayin da yake maganar, Mi...