Da Sunan Alah mai rahama mai jinkai, dukan yabo da girmamawa sun tabbata ga Allah ubangijin talikai.
Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma Annabi Muhammad(SAW) Manzonsa ne.
Shin ka taba yin Zina, kana da niyyar yi bisa sanin cewa haramun ce amma ka tuba daga baya?
Shin Allah yana yafe laifin Zina idan aka tuba?
Zina na daya daga cikin manyan laifuka a addinin musulunci.
Allah madaukakin sarki ya fada mana a Qur'ani cewa,' Kada ku kusanci Zina, Alfashace kuma hanya ce ta shedan' Qur'an 17:32.
Hakanan kuma Allah madaukakin sarki na cewa
'Kuma Wadannan da basu hada Allah da wani ba wajan bauta, basu kashe ran da Allah ya hana a kashe ba, saidai bisa gaskiya, kuma basu aikata Zina ba. Amma duk wanda ya aikata haka, zai gamu da Azaba. Zai gamu da Azaba n...