Tuesday, December 16
Shadow
DA ƊUMIƊUMINSA: Ɗan Gidan IBB Ya Ki Karɓar Sabon Muƙamin Shugaban Bankin Manoma Da Tinubu Ya Ba Shi

DA ƊUMIƊUMINSA: Ɗan Gidan IBB Ya Ki Karɓar Sabon Muƙamin Shugaban Bankin Manoma Da Tinubu Ya Ba Shi

Duk Labarai
Daga Muhammad Kwairi Waziri Mohammed Babangida, ɗan tsohon shugaban ƙasa Janar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB), ya yi watsi da nadin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya masa a matsayin Shugaban Bankin Manoma na Najeriya (BOA). Majiyoyi sun tabbatar da cewa Mohammed ya bayyana rashin amincewarsa da muƙamin, yana mai cewa wasu dalilai na sirri da kuma tsare-tsaren kansa ne suka sa ya yanke shawarar kin karɓa, duk da girmansa. Nadin nasa ya kasance cikin jerin sabbin nade-naden da shugaban ƙasa ke yi domin farfaɗo da harkokin noma da bunkasa rayuwar manoma a ƙasar nan. Sai dai wannan mataki da Mohammed ya ɗauka na watsi da mukamin ya janyo cece-kuce a kafafen sada zumunta da cikin ‘yan siyasa. Har yanzu babu wata sanarwa kai tsaye daga fadar shugaban ƙasa ko daga bakin Mohammed Baban...
Kotu ta hana tsohon Gwamnan jihar Kogi, Yahya Bello Fasfo dinsa inda yace yana son ya je kasar waje a duba lafiyarsa, Saidai kotun tace bai bayar da hujjar cewa Likitocin Najeriya ba zasu iya magance rashin lafiyar tashi ba

Kotu ta hana tsohon Gwamnan jihar Kogi, Yahya Bello Fasfo dinsa inda yace yana son ya je kasar waje a duba lafiyarsa, Saidai kotun tace bai bayar da hujjar cewa Likitocin Najeriya ba zasu iya magance rashin lafiyar tashi ba

Duk Labarai
Babbar Kotun tarayya dake Maitama Abuja ta hana tsohon gwamnan jihar Kogi Yahya Bello Fasfo dinsa dan ya je kasar waje neman magani. Mai shari'a Justice Emeka Nwite ya bayyana wannan hukunci. Yace takardun da Tsohon gwamnan ya gabatar na neman ya tafi kasar ingila basu da tambarin sarki wanda kotun tace basu da wani amfani a wajanta. Dan haka tace kuma rashin lafiyar ta tsohon gwamnan ba ta yi tsananin da za'a ce sai an fitar dashi kasar waje ba. Ana zargin tsohon gwamnan da dan uwansa, Ali Bello, Dauda Suleiman da Abdulsalam Hudu wajan satar Naira N80, 246,470, 088.88.
Da gaske an soke jarabawar WAEC ta 2025 saboda yawan satar amsa? Hukumar jarabawar ta yi karin bayani

Da gaske an soke jarabawar WAEC ta 2025 saboda yawan satar amsa? Hukumar jarabawar ta yi karin bayani

Duk Labarai
Hukumar shirya jarabawar kammala sakandare ta WAEC ta yi martani kan labarin da ke cewa an soke jarabawar ta shekarar 2025. Labarai na ta jawo a kafafen sadarwa inda aka ji wasu na cewa an soke jarabawar ta shekarar 2025. An bayyana cewa an soke jarabawar ne saboda yawaitar satar amsa. Saidai hukumar ta WAEC a Martani kan lamarin tace bata soke jarabawar ba asali ma nan da watan Augusta zata saki sakamakon jarabawar. “The attention of the West African Examinations Council (WAEC), Nigeria, has been drawn to a press statement alleging the cancellation of all the papers written during the just concluded WASSCE for School Candidates, 2025. According to the press statement dated Saturday, July 19, 2025, being circulated on social media platforms, the Federal Ministry of Education, ...
Kotu ta daure mutane 2 a gidan yari saboda sare itace a Kano

Kotu ta daure mutane 2 a gidan yari saboda sare itace a Kano

Duk Labarai
Kotu dake Normansland a Kano ta daure mutane 2 bisa hannu a sare itace a jihar wanda sabawa dokar Muhalli ta jihar ne. Ma'aikatar Muhalli ta jihar, ta sanar da cewa an kama wani me suna Salihu Mukhtar da wani abokin aikinsa da suka sare itace akan titin Jigawa Road dake Nasarawa GRA. Lauya me gabatar da kara, Barrister Bahijjah Aliyu ne ya gayawa kotu cewa wadanda aka kama din sun karya dokar muhalli ta jihar. An yankewa daya daga cikinsu hukuncin daurin watanni 3 a gidan yari ko biyan tarar Naira 20,000. Sannan aka yankewa dayan hukuncin daurin watanni 6 a gidan yari ko biyan tarar Naira dubu 50. Kwamishinan muhalli na jihar, Dr. Dahiru Hashim ya bayyana cewa ba zasu amince da sare itatuwa a jihar ba.
Dala Biliyan $3.6 ‘yan Najeriya suka rika kashewa duk shekara wajan zuwa kasashen waje neman magani a zamanin Buhari

Dala Biliyan $3.6 ‘yan Najeriya suka rika kashewa duk shekara wajan zuwa kasashen waje neman magani a zamanin Buhari

Duk Labarai
.Rahotanni sun ce a zamanin mulkin tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari 'yan Najeriya sun kashe jimullar dala Biliyan $29.29 wajan zuwa kasashen waje neman magani. Hakan na nufin 'yan Najeriya sun rika kashe akalla dala $3.6 duk shekara wajan neman magani a kasashen waje a shekaru 8 da tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya yi yana mulki. Hakan ya bayyana ne daga bayanan da babban bankin Najeriya, CBN ya fitar. Hakan ya nuna irin yanda 'yan Najeriya suka dogara da kasashen waje wajan neman magani.
Hotuna Da Duminsa: Kwankwaso ya je ganawa da shugaba Tinubu a Abuja

Hotuna Da Duminsa: Kwankwaso ya je ganawa da shugaba Tinubu a Abuja

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":["local"],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{"square_fit":1},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":true,"containsFTESticker":false} Tsohon gwamnan jihar Kano, kuma jigon jam'iyyar NNPP Sen. Rabiu Musa Kwankwaso, yanzu haka yana fadar shugaban kasa domin ganawa shugaban kasa Tinubu
ADC ce ke amfani da rasuwar Buhari don neman karɓuwa ba ji ba>>Shugaba Tinubu

ADC ce ke amfani da rasuwar Buhari don neman karɓuwa ba ji ba>>Shugaba Tinubu

Duk Labarai
Fadar Shugaban Najeriya ta mayar da martani kan zargin da jam’iyyar haɗaka ta ADC ta yi na cewa gwamnatin shugaba Bola Tinubu na amfani da rasuwar tsohon shugaba Muhammadu Buhari, don samun tagomashi na siyasa da neman karɓuwa a idon jama'a. Mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labarai, Sunday Dare ya bayyana zargin na ADC a matsayin “abin kunya,” inda ya ce jam’iyyar ce ke amfani da rasuwar Buhari don neman suna. ADC dai ta ce gwamnatin Tinubu ta yi amfani da yadda aka gudanar da jana’izar Buhari da kuma yadda aka shirya bikin bankwana da shi a Daura da ke jihar Katsina, domin ƙara samun ƙarbuwa a idon ƴan ƙasa. Fadar shugaban ƙasar ta ce marigayi Muhammadu Buhari ya cancanci yi masa jana'izar ban-girma kuma sun yi haka ne don girmamawa saboda hakan ne ya dace da sh...
YANZU-YANZU: An Fara Gudanar Da Zàñga-zàñgar Kan Karin Albashi Da Fanshøɲ ‘Yan Sanda Masu Aiki Da Masu Ritaya

YANZU-YANZU: An Fara Gudanar Da Zàñga-zàñgar Kan Karin Albashi Da Fanshøɲ ‘Yan Sanda Masu Aiki Da Masu Ritaya

Duk Labarai
YANZU-YANZU: An Fara Gudanar Da Zàñga-zàñgar Kan Karin Albashi Da Fanshøɲ 'Yan Sanda Masu Aiki Da Masu Ritaya. Daga Muhammad Kwairi Waziri Yayin wata gagarumar zanga-zanga da aka gudanar a yau, Omoyele Sowore, ɗan gwagwarmaya kuma tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa, ya jagoranci gungun masu zanga-zanga domin neman a inganta rayuwar jami’an ‘yan sanda a Najeriya. Masu Zãɲgà-Zàɲģà sun bukaci gwamnati ta duba halin kuncin da ‘yan sanda ke fuskanta, musamman yadda albashinsu ke ƙasa da kima, tare da rashin kula da ‘yan sanda da suka yi ritaya. Sun ce lokaci ya yi da za a mutunta waɗanda ke bayar da rayukansu don kare lafiyar jama’a da dukiyarsu. Sowore ya bayyana cewa, "Yan sanda su ne ginshiƙin tsaro a ƙasa, amma ana wulaƙanta su da iyalansu. Ba za mu ci gaba da shiru ba alhali ...