‘Ba mu cire arewa maso yamma cikin waɗanda za su ci gajiyar wankin ƙoda ba’>>Inji Gwamnatin Tarayya
Ma'aikatar lafiya ta tarayya ta musanta rahotanni da ke cewa babu marasa lafiya daga arewa maso yamma cikin waɗanda za su ci gajiyar shirin rage farashin wankin ƙoda da gwamnatin ƙasar ta amince da shi ba.
Wata sanarwa da ma'aikatar ta wallafa a shafinta na X, ta ce labarin ba shi da kamshin gaskiya.
Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ne dai ya amince da rage farashin wankin ƙoda a manyan asibitocin tarayya a faɗin ƙasar.
Karkashin tsarin, za a rage farashin wankin ƙoda daga naira 50,000 zuwa naira 12,000.
Shirin wanda aka ɓullo da shi karkashin shirin Renewed Hope na kyautata rayuwar ƴan Najeriya, yana cikin ƙoƙari da gwamnatin tarayya ke yi wajen rage wa masu fama da cutukan da suka jiɓanci ƙoda raɗaɗi.
An fara shirin ne a manyan asibitocin tarayya guda 11 a faɗin ƙasar.
As...








