Wednesday, March 4
Shadow
KALLI INDA RANKA: Matashi Ya Sadaukar Da Soyayyar Budurwarsa ta Shekaru 8 Akan Sabon LIFAN Da 200k

KALLI INDA RANKA: Matashi Ya Sadaukar Da Soyayyar Budurwarsa ta Shekaru 8 Akan Sabon LIFAN Da 200k

Duk Labarai
INDA RANKA: Matashi Ya Sadaukar Da Soyayyar Budurwarsa ta Shekaru 8 Akan Sabon LIFAN Da 200k Kamar Yadda Muka Samu Rahoto Wani Attajiri ne ya nuna bukatar matashin Yabar masa budurwarsa da suke soyayya domin ya aure ta, inda yanajin tayin attajirin matashin baiyi wata-wata ba ya karba, yayi bakwana da Ita nan take. Shin kuma zaku iya Hakan?
Bidiyo: Babu Wahala a Jihar Naija, Kuma kowacw jiha a Arewa ta shaida ci gaban da shugaba Tinubu ya kawo>>Inji Gwamnan jihar Naija

Bidiyo: Babu Wahala a Jihar Naija, Kuma kowacw jiha a Arewa ta shaida ci gaban da shugaba Tinubu ya kawo>>Inji Gwamnan jihar Naija

Duk Labarai
Gwamnan Jihar Naija, Umar Bago ya bayyana cewa, Babu Wahala a jihar Naija. Yace farashin kayan abinci sun saika, Ana noma sosai sannan yana gina tituna. Da aka tambayeshi kan Sauran jihohin Arewa dake kuka da tsare-tsaren Gwamnatin Tinubu, sai yace babu jihar da Tsare-tsaren Gwamnatin Tinubu ba su kai ci gaba ba. https://www.tiktok.com/@madubitv2790/video/7540384826646334725?_r=1&u_code=ejaikd8elj8058&preview_pb=0&sharer_language=en&_d=ejaij098emc1h5&share_item_id=7540384826646334725&source=h5_m&timestamp=1755785973&user_id=7483197776647635989&sec_user_id=MS4wLjABAAAAN7fVbcc0mzRzgIxdVwTekj-Bzgfq381B8aILPWs15fqP6aFNZ5GwIpbLEwMTYvVW&social_share_type=0&utm_source=copy&utm_campaign=client_share&utm_medium=android&share_iid=7510...
Gidajen Man fetur din Najeriya A.A Rano, Total, Mobil, sun rage farashin man fetur dinsu a Abuja

Gidajen Man fetur din Najeriya A.A Rano, Total, Mobil, sun rage farashin man fetur dinsu a Abuja

Duk Labarai
Gidajen man fetur din Najeriya irin su AA Rano, Total, Mobil, NIPCO duk sun rage farashin man fetur dinsu dan yin gasa da kamfanin man fetur na kasa, NNPCL da sauransu. Saidai ragin ya farune a Abuja da kewaye kadai. Gidajen man fetur din AA Rano, Ranoil, Mobil, da NIPCO sun rage farashin man su zuwa Naira 890 akan kowace lita maimakon Naira 945. Suma gidajen man fetur din Empire Energy, Emadab, da Total duk sun rage farashin man fetur dinsu inda wasu ke sayarwa akan naira 899 wasu kuma 910 akan kowace lita a Abuja. Shugaban kungiyar 'yan kasuwar, Abubakar Maigandi ya bayyana cewa sun rage farashinne saboda faduwar farashin danyen man fetur da kuma raguwar farashin man a inda suke sarowa.
Gwamnatin tarayya ta yi karin haske kan dalilin da yasa ba’a ga kowa ba a wajan da aka warewa Najeriya a taron kasashen Duniya a kasar Japan

Gwamnatin tarayya ta yi karin haske kan dalilin da yasa ba’a ga kowa ba a wajan da aka warewa Najeriya a taron kasashen Duniya a kasar Japan

Duk Labarai
Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa, Dalilin da yasa ba'a ga kowa ba a wajan da aka warewa Najeriya a wajan taron ci gaban kasashen Afrika a kasar Japan ba, wakilan Najeriya sai ranar Alhamis zasu isa wajan. Rahotanni sun watsu cewa, babu wakilin Najeriya a wajan inda sai wani dan Najeriya ne da ya halarci taron kuma abin bai masa dadi ba ya gabatar da kansa a matsayin shine ke wakiltar kasar. Saidai a bayanin me magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga, yace Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya halarci wajan taron, Bankin masana'antu, Bank of industry ya halarci wajan taron, Ministan wuta, da sauran manyan ma'ikatan gwamnati duk dun halarci wajan taron amma duk suna can suna ganawa da wakilan kasuwanci da zai amfani Najeriya. Ya kara da cewa, wadanda zasu tsaya a wajan da ak...
Da Duminsa: Bayan Kiraye-Kiraye, Gwamnatin Tarayya ta saka Asibitin Aminu Kano cikin wadanda aka yi ragin wankin Koda daga Naira dubu 50 zuwa Naira Dubu 12

Da Duminsa: Bayan Kiraye-Kiraye, Gwamnatin Tarayya ta saka Asibitin Aminu Kano cikin wadanda aka yi ragin wankin Koda daga Naira dubu 50 zuwa Naira Dubu 12

Duk Labarai
Zuwa yanzu dai an saka Asibitin Malam Aminu Kano dake Kano cikin asibitocin gwamnatin tarayya ta aka yi ragin wankin Koda daga Naira dubu 50 zuwa Naira dubu 12. A baya dai an samu suka ga gwamnati bayan data sanar da ragin kudin wankin kodar a asibitocin Gwamnatin tarayya ba tare da hadawa da asibitin malam Aminu Kano ba. Lamarin ya jawo cece-kuce sosai musamman a kafafen sada zumunta. Saidai a cewar tsohon Hadimin Gwamnan Kano, Abubakar Aminu Ibrahim ya bayyana cewa, yanzu an saka Asibitin malam Aminu Kano cikin wadanda akawa ragin.
DA ƊUMI-ƊUMI: Ɗan Nijeriya ya zo na 3 a gasar Musabaƙar Al-ƙur’ani ta Duniya

DA ƊUMI-ƊUMI: Ɗan Nijeriya ya zo na 3 a gasar Musabaƙar Al-ƙur’ani ta Duniya

Duk Labarai
Ɗan Nijeriya ya zo na 3 a gasar Musabaƙar Al-ƙur'ani ta Duniya Bukhari Sunusi Idris ɗan asalin jihar Kano da ya wakilci Nijeriya gasar Musabaƙar Al-ƙur'ani ta duniya, ya samu nasarar zuwa mataki na uku, a ɓangaren Izu Sittin da Tafsir. Hakazalika ya samu kyautar Riyal dubu 400, wanda ya kai kwatankwacin Naira Miliyan 160. Gasar wadda aka gudanar a kasar Saudiyya. Wane fata kuke masa?
Kalli Hotunan dan Peter Obi da ake rade-radin dan Lùwàdì ne

Kalli Hotunan dan Peter Obi da ake rade-radin dan Lùwàdì ne

Duk Labarai
Hotunan dan Peter Obi me suna Oseloka Obi sun bayyana a kafafen sadarwa inda ake ta rade-radin cewa dan Luwadi ne. Oseloka Obi na zaunene a kasar Ingila kuma dan fim ne. IWasu magoya bayan Peter Obi na cewa ba gaskiya bane saboda Oseloka Obi dan fim ne kuma hotunan da akw yadawa ba na gaskiya bane. Zuwa yanzu dai babu wata sanarwa daga Oseloka Obi ta tabbatarwa ko karyata wannan ikirari.