Barr. Abba Hikima Fagge: “Shugabannin siyasa ne ke hura wutar faɗan daba a Kano”
Barr. Abba Hikima Fagge: "Shugabannin siyasa ne ke hura wutar faɗan daba a Kano"
Fitaccen lauya kuma mai sharhi kan al’amuran yau da kullum a Kano, Barrister Abba Hikima Fagge, ya yi tsokaci kan matsalar fadan yan daba da ke ta ƙara ƙaruwa a cikin birnin Kano. A cewarsa, ba matasa da kansu ne tushen wannan matsala ba, sai dai shugabannin siyasa da ke amfani da su wajen cimma muradunsu.
Barr. Abba ya bayyana cewa, a lokutan siyasa musamman, ana yawan ganin yadda ake rarraba kuɗi da miyagun ƙwayoyi ga matasa domin a tura su wajen tada tarzoma, abin da daga ƙarshe yake jefa al’umma cikin tsoro da rashin kwanciyar hankali.
Ya ƙara da cewa, “Matsalar daba ba sabon abu ba ne a Kano, amma abin takaici shi ne yadda shugabannin da ake ɗora ran samun mafita a kansu suke ƙara ƙara wa mat...








