Kalaman godiya ga saurayi
Idan saurayinki ya miki kyauta, yana da kyau ki gode masa hakan zai kara bashi karfin gwiwar sake yi miki wata kyautar nan gaba.
Ga kalaman Godiya ga Saurayi kamar haka:
Nagode sosai Allah yasa ka fi haka.
Allah saka maka da Mafificin Alheri.
Kyauta na daga cikin alamun soyayya, a kullun kana kara nuna min irin yanda ka damu dani, nagode da wannan kyauta.
Ka sakani cikin farin ciki sosai, fatana shine Allah ya bani ikon faranta maka nima.
Baka gajiya da yi min kyauta, hakan na kara narkar dani a cikin soyayyarka.
Kamin kyautar da ban taba tunin samu ba, ban da kalaman da zan iya nuna cikakkiyar godiya ta gareka, dan haka kawai zance Allah saka maka da Alheri.
Wanda ya damu da kai shi ke maka kyauta, na gode da damuwa dani.
Kyautarka na kara tabbatar min da zaka m...

