Allah Sarki: Kalli Bidiyon yanda Paul Pogba ke kuka bayan Komawa kungiyar AS Monaco
Paul Pogba ya saka hannun yarjejeniya da kungiyar AS Monaco.
Zai bugawa kungiyar wasa na tsawon shekaru 2 zuwa shekarar 2027.
Hakan na zuwane bayan da ya kammala dakatarwar shekaru 2 da aka masa bayan samunshi da ta'ammuli da miyagun kwayoyi.
https://twitter.com/NigeriaStories/status/1939052855815741547?t=K6H25L7HO2F_6YNje1ZAIA&s=19
Da farko an yanke masa dakatarwar shekaru 4 amma daga baya aka mayar dashi shekaru 2 bayan ya daukaka kara.
Saidai Pogba a yayin da yake sakawa AS Monaco hannu ya fashe da kuka inda aka rika bashi baki.








