Wednesday, December 24
Shadow
Ji sabon mukamin da Shugaba shugaba Tinubu ya baiwa Ganduje bayan sauka daga shugaban APC

Ji sabon mukamin da Shugaba shugaba Tinubu ya baiwa Ganduje bayan sauka daga shugaban APC

Duk Labarai
Rahotanni sun ce shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu na shirin baiwa tsohon shugaban jam'iyyar APC, Dr. Abdullahi Umar Ganduje sabon mukami. Hakan na zuwane kwana daya da saukat Ganduje daga mukamin shugaban jam'iyyar APC. Wata majiya ta bayyanawa jaridar Vanguard cewa, Shugaban kasa Bola Tinubu kwanannan zai bayyana Ganduje a matsayin jakadan Najeriya zuwa kasar waje. A kwanakin baya dama an yada rade-radin cewa, Shugaba Tinubu na shirin baiwa Ganduje mukamin jakadanci amma maganar ta lafa. Wasu majiyoyi sun ce Ganduje a wancan lokacin ya ki karbar mukamin jakadane saboda yana jan zarensa a matsayin shugaban jam'iyyar APC wanda yana ganin kujerar shugaban jam'iyya tafi karfin ta Jakada. Da yawa a wancan lokaci sun yi mamakin irin karfin da Ganduje ke dashi a gwamnatin Tinubu ...
Mun yi babban rashi>>Shugaba Tinubu ya gayawa yi jimamin rasuwar Dantata

Mun yi babban rashi>>Shugaba Tinubu ya gayawa yi jimamin rasuwar Dantata

Duk Labarai
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya yi jimamin rasuwar Aminu Dogo Dantata a sakon da ya fitar ta bakin kakakinsa, Bayo Onanuga. Shugaban yace wannan rashi ne da Najeriya ta yi baki daya. Yace za'a tuna Dantata da kasuwancin da yayi da kuma taimakawa da yayi wajan hadin kan Najeriya ta wajan bayar da tallafin da ya amfani mutane da yawa. Tinubu ya bayyana Dantata a matsayin mutumin da ya bashi gudummawa wajan shawara me kyau. A karshe ya mikawa iyalan mamacin sakon ta'aziyya.
Dalori ya maye gurbin Ganduje a matsayin shugaban APC na riƙo

Dalori ya maye gurbin Ganduje a matsayin shugaban APC na riƙo

Duk Labarai
Mataimakin shugaban jam'iyyar APC na yankin arewa, Ali Bukar Dalori ya maye gurbin Abdullahi Umar Ganduje a matsayin shugaban jam'iyyar na riƙo. Wannan na zuwa ne bayan tsohon gwamnan na jihar Kano ya ajiye muƙamin a ranar Juma'a, sannan aka naɗa Dokta Ali Bukar Dalori a matsayin wanda zai riƙe muƙamin, kafin a kai ga zaɓen wanda zai maye gurbinsa. Mutane dai sun yi zargin ruwa ba ya tsami banza, ko kuma dai da walakin goro a miya amma uwar jam'iyyar ta yi watsi da wannan hasashe. Bala Ibrahim shi ne daraktan yaɗa labarai na jam'iyyar ta APC, ya ce "Game da batun wanda zai maye gurbin shugaban jam'iyyar da sauka, dama jam'iyya na da kundin tsarin mulki wanda ya yi tanadi irin wannan wanda idan shugaban jam'iyya ya sauka daga muƙaminsa to za a zaɓi ɗaya daga cikin mataimakansa biyu...
Ji dalilin da ya sa yawanci shugabannin jam’iyyu a Najeriya ke sauka ba girma ba arziki?

Ji dalilin da ya sa yawanci shugabannin jam’iyyu a Najeriya ke sauka ba girma ba arziki?

Duk Labarai
A ranar Juma'a ne shugaban jam'yyara APC na Najeriya, Abdullahi Umar Ganduje ya a jiye muƙaminsa na jangorancin jam'iyyar. Tsohon gwamnan jihar Kanon ya sauka da muƙamin nasa ne bayan shafe kusan shekara biyu riƙe da shugabancin jam'iyyar a matsayin riƙo bayan saukar Sanata Abdullahi Adamu. Wasu majiyoyi daga fadar shugaban Najeriya sun tabbatar wa BBC cewa Ganduje ya ajiye muƙamin ne bayan da fadar shugaban ƙasa ta umarce shi da yin hakan. "Da gaske ne Ganduje ya sauka tun ranar Alhamis aka ba shi umarnin ya rubuta takardar murabus, a ranar Juma'a da safe miƙa takardar," in ji majiyar. Kusan a iya cewa ya zama al'ada a tsarin siyasar Najeriya kusan duka mutanen da suka jagoranci manyan jam'iyyun ƙasar ba sa wanyewa lafiya da muƙaman nasu. Wasu daga cikinsu ana dakatar da su...
Karanta Jadawalin tsaffin shuwagabannin jam’iyyar APC da aka taba yi

Karanta Jadawalin tsaffin shuwagabannin jam’iyyar APC da aka taba yi

Duk Labarai
Wannan jadawalin shuwagabannin jam'iyyar APC ne da aka taba yi daga shekarar 2013 zuwa yanzu. 1. Chief Bisi Akande: 2013 - 20142. Chief John Odigie-Oyegun: 2014 - 20183. Comrade Adams Oshiomhole: 2018 - 20204. Mai Mala Buni: 2020 - 20225. Senator Abdullahi Adamu: 2022 - July 20236. Senator Abubakar Kyari (Acting). July 2023 - Aug 20237. Dr. Abdullahi Ganduje: 2023-2025.
Tinubu Ya Naɗa Tsohon Hadimin Buhari Shugaban PCNGi

Tinubu Ya Naɗa Tsohon Hadimin Buhari Shugaban PCNGi

Duk Labarai
Shugaba Bola Tinubu ya naɗa Ismael Ahmed, tsohon hadimin tsohon Shugaba Muhammadu Buhari, a matsayin Shugaban Hukumar Presidential Compressed Natural Gas Initiative (PCNGi). Wannan shiri na gwamnati na da nufin rage radadin cire tallafin fetur ta hanyar samar da makamashi mai araha da tsafta. Ismael Ahmed ya kasance mai ba Buhari shawara kan Shirin Tallafin Jama'a tsakanin 2018 zuwa 2022. Ya kammala karatunsa na lauya a Jami’ar Abuja, sannan ya samu digirin digirgir a fannin Hulɗar Ƙasashen Duniya daga Jami’ar Webster da ke Amurka.
Da Duminsa: Kasar Faransa ta haramta shan taba a bainar jama’a

Da Duminsa: Kasar Faransa ta haramta shan taba a bainar jama’a

Duk Labarai
Kasar Faransa ta Haramta shan taba sigari a bainar jama'a. Kasar tace ta haramta shan taba a wajan shakatawa dake gabar tekuna da wajan jiran ababen hawa da sauransu. Tun a baya dai kasar take ta bayyana aniyar son hana shan taba amma sai wannan karin ta samu nasarar aiwatar da aniyarta. Rahotanni na bayabayannan sun ce akalla mutane miliyan 7 ne ke mutuwa saboda taba sigari a Duniya.
Talakawa na karuwa sosai a Najeriya, mutane da yawa basa samun Naira dubu biyar a rana>>Inji Bankin Duniya

Talakawa na karuwa sosai a Najeriya, mutane da yawa basa samun Naira dubu biyar a rana>>Inji Bankin Duniya

Duk Labarai
Bankin Duniya ya bayyana cewa, Talakawa na karuwa sosai a Najeriya dama wasu sauran kasashe 38 na Duniya. Bankin yace hakane a wani babban rahoto da ya fitar tun bayan bullar cutar Korona a shekarar 2020. Bankin yace jimullar mutane Miliyan 421 ne ke fama da matsanancin talauci a Duniya. Bankin ya kara da cewa, mutanen basa samun akalla Dala $3 a kullun wanda kwatankwacin Naira dubu biyar kenan. Bankin ya alakanta hakan da matsalolin tsaro da sauransu. Ya kuma yi gargadin yawan matalautan na iya karuwa zuwa mutane Miliyan 435 nan da shekarar 2030.