Thursday, March 5
Shadow
Matashiya ‘Yar Asalin Jihar Yobe, Nafisa Abdullahi Ta Lashe Gasar Turanci Ta Duniya

Matashiya ‘Yar Asalin Jihar Yobe, Nafisa Abdullahi Ta Lashe Gasar Turanci Ta Duniya

Duk Labarai
Matashiya 'Yar Asalin Jihar Yobe, Nafisa Abdullahi Ta Lashe Gasar Turanci Ta Duniya. Nafisa Abdullah Aminu, yarinya ‘yar shekaru 17 daga jihar Yobe, ta samu babban nasara a gasar ƙasa da ƙasa ta harshen Turanci da aka gudanar a London, Birtaniya, ƙarƙashin TeenEagle Global Finals 2025. Nafisa, wadda ke karatu a Nigerian Tulip International College (NTIC), Yobe, ta fice daga cikin fiye da ɗalibai 20,000 daga ƙasashe 69 – ciki har da waɗanda harshen Turanci ke matsayin na uwa-uba a wurinsu. Wannan gagarumar nasara da ta samu ana kallonta a matsayin abin alfahari ga Najeriya da nahiyar Afrika gaba ɗaya, duba da asalin jihar da ta fito wadda ke fama da ƙalubale a harkar ilimi da tsaro. A sakamakon haka, hukumomi da malamai a jihar Yobe sun nuna farin ciki da wannan nasara, suna...
Ina nan da raina, Samha M. Inuwa ta karyata rade-radin da ake yadawa akanta bayan hadarin data yi

Ina nan da raina, Samha M. Inuwa ta karyata rade-radin da ake yadawa akanta bayan hadarin data yi

Duk Labarai
Tauraruwar fina-finan Hausa, Samha M. Inuwa ta karyata rade-radin da ake yadawa na cewa ta mutu. Samha a sanarwar data fitar ta shafinta tace ta fito ta sanar da mutanene cewa, tana samun sauki kuma ba kamar yanda wasu ke yadawa ba cewa wai ta mutu, tace tana nan da ranta. Ta yi godiya da 'yan uwanta da abokan sana'arta da masoya da suka nuna damuwa game da abinda ya sameta. https://www.tiktok.com/@samha_m_inuwa/video/7534750431516380421?_t=ZS-8ybcxZqQPWT&_r=1
Kada ma ka yi tunanin tsayawa takarar shugaban kasa a 2027 dan ba zaka ci ba>>Wata Kungiyar Yarbawa ta gayawa shugaba Tinubu

Kada ma ka yi tunanin tsayawa takarar shugaban kasa a 2027 dan ba zaka ci ba>>Wata Kungiyar Yarbawa ta gayawa shugaba Tinubu

Duk Labarai
Wata Kungiyar Yarbawa me suna Ìgbìnmó Májékóbájé Ilé-Yorùbá ta bayyana cewa, Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya gaza a fannin inganta tattalin arziki da samar da tsaro. Kungiyar a sanarwar data fita daga bakin shugaban ta, Olusola Badero wanda me magana da yawunta, Princess Balogun ya fitar. Yace Talauci musamman a yankin Yarbawa ya karu hakanan matsalar tsaro ta karu. Ya kawo misalin cewa kwanannan aka sace wasu manoma a yankin inda sai da danginsu suka tara kudi sannan aka sakesu. Yace Tinubu ya kasa cika Alkawuran da ya dauka, dan haka yace Aso Rock ba gidan gado bane, kada ma Tinubu yayi tunanin tsayawa takara a 2027 dan ba ci zai yi ba.
WAEC ta fitar da sakamakon jarrabawar 2025

WAEC ta fitar da sakamakon jarrabawar 2025

Duk Labarai
Hukumar shirya jarrabawar kammala sakandire ta Afirka ta Yamma, WAEC ta fitar da sakamakon jarrabawar 2025 a Najeriya. Cikin wata sanarwa da hukumar ta wallafa a shafinta na X, ta ce ta saki sakamakon ne a yau Litinin 4 ga watan Agustan 2025. Hukumar ta kuma buƙaci ɗaliban da suka rubuta jarrabawar da su shiga shafinta na http://waecdirect.org. domin duba sakamakon jarrabawar tasu.
Suma ‘yan Kwallon Kwando mata Shugaba Tinubu ya baiwa kowaccensu kyautar Naira Miliyan 150 da gidaje

Suma ‘yan Kwallon Kwando mata Shugaba Tinubu ya baiwa kowaccensu kyautar Naira Miliyan 150 da gidaje

Duk Labarai
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya ba ƴan wasan kwandon Najeriya mata dala 100,000 da lambar girma ta OON saboda nasarar da suka samu ta lashe kofin gasar kofin Afirka ta wato Afrobasket. Shugaban ya kuma ba masu horar da ƴanwasan dala 50,000 kowannensu. hakanan kowannensu an bata kyautar gida hadda masu horas dasu. Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ne ya bayyana hakan a madadin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu. Wannan na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan shugaban ya ƴanwasan ƙwallon ƙafa mata kyautar dala 100,000 da lambar girma.
Kalli Bidiyo: Ko Sheik Alkali Zaria Ya Aure Ni Ko Kuma Na Balle Na Shiga Yawon Duniyà A Lagos, Cewar Murja Kunya

Kalli Bidiyo: Ko Sheik Alkali Zaria Ya Aure Ni Ko Kuma Na Balle Na Shiga Yawon Duniyà A Lagos, Cewar Murja Kunya

Duk Labarai
Ko Sheik Alkali Zaria Ya Aure Ni Ko Kuma Na Balle Na Shiga Yawon Duniyà A Lagos, Cewar Murja Kunya Murja ta bayyana cewa tana matukar kaunar Shehin Malamin ne saboda yadda yake tsage gaskiya komi dacinta. https://www.tiktok.com/@murjakunya0/video/7534121202378411269?_t=ZS-8ybH6O8W7IO&_r=1 Lamarin ya dauki hankula sosai.
Tawagar ƴan matan wasan kwandon Najeriya ta isa gida bayan lashe kofin Afirka

Tawagar ƴan matan wasan kwandon Najeriya ta isa gida bayan lashe kofin Afirka

Duk Labarai
Tawagar ƴan wasan ƙwallon kwando mata ta Najeriya ta koma ƙasar bayan lashe gasar ƙwallon ƙwando ta mata ta Afirka. Tawagar ta D’Tigress ta samu gagarumar tarba daga masoya ƙwallon ƙwanda a Najeriya, lokacin da suka sauka a filin jirgin sama na Abuja. Ministar Mata Iman Sulaiman Ibrahim da takwararta ta al'adu, Hannatu Musawa ne suka yi wa tagawar rakiya tun daga birnin Abidjan zuwa Abuja. A ranar Lahadi ne tawagar D’Tigress ta lashe gasar ƙwallon ƙwando ta tama ta Afirka, bayan doke Mali da ci 78-64. Wannan ne karo na bakwai da tawagar Najeriya ta lashe kofin gasar a tarihi, wanda kuma shi ne na biyar a jere da ta ɗauka.
Ƴan canji a Abuja sun dakatar da ayyuka don tantance masu sana’ar

Ƴan canji a Abuja sun dakatar da ayyuka don tantance masu sana’ar

Duk Labarai
Haɗakar ƙungiyar masu canjin kuɗaɗen ƙasar waje ta Abuja ta dakatar da ayyukanta domin tantance ma'aikatanta. Shugaban ƙungiyar Alhaji Salisu Umar ya shaida wa BBC cewa sun ɗauki matakin ne domin tsaftace kasuwar. Ya ce dama sukan yi haka lokaci zuwa lokaci domin tabbatar da ingancin sana'ar tasu. Wakiliyar BBC da ta ziyarci kasuwar da ke unguwar Zone 4 a tsakiyar birnin Abuja, ta ce duka shaguna manya da ƙanana a kasuwar sun kasance a rufe.
Gwamnatin Kano ta karɓi rahoton binciken kwamishinan da ake zargi da belin Danwawu

Gwamnatin Kano ta karɓi rahoton binciken kwamishinan da ake zargi da belin Danwawu

Duk Labarai
Kwamitin da gwamnatin jihar Kano ta kafa domin binciken zargin kwamishinan sufurin jihar Ibrahim Namadi da hannu a belin mutumin da ake zargi da safarar miyagun ƙwayoyi a jihar ya miƙa wa gwamnati rahotonsa. A yau Litinin ne kwamitin ƙarƙashin jagorancin Barrister Aminu Hussaini ya miƙa rahoton binciken nasa ga sakataren gwamnatin jihar. Babu dai cikakken bayanin abin da rahoton ya ƙunsa, to sai dai matakin da gwamnati za ta ɗauka ne zai fayyace abin da kwamitin ya gano a binciken nasa. A makon da ya gabata ne dai gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya kafa kwamitin, bayan da aka zargi Namadi da ƙarbar belin Danwawu, mutumin da ake zargi da dillancin miyagun ƙwayoyi. Batun ya janyo zazzafar muhawara a ciki da wajen jihar, inda wasu ke ganin bai kamata mutum mai matsayi irin na...
Gwamnatin Kano za ta mayar da gidan yarin Kurmawa gidan tarihi

Gwamnatin Kano za ta mayar da gidan yarin Kurmawa gidan tarihi

Duk Labarai
Gwamnatin jihar Kano ta ɓullo da shirin mayar da gidan yarin Kurmawa - da ya kwashe shekara fiye da 100 - gidan tarihi domin adana abubuwan da suka faru lokacin mulkin mallaka. Gidan yarin mai shekara 115, an gina shi ne lokacin Turawan mulkin mallaka a kusa da fadar sarkin Kano domin a riƙa ɗaure masu laifi a ciki. A bisa ƙa'idar da aka gina gidan yarin Kurmawa zai ɗauki fursunoni 690 ne kawai Mai bai wa gwamnan jihar Kano shawara kan harkokin yaɗa labara, Ibrahim Adam ne ya bayyana haka a shafinsa na Facebook. Ibrahim Adam ya ce za a mayar da fursunonin da ke ɗaure a gidan yarin zuwa sabon gidan fursunan Janguza na zamani, da ke kusa da barikin soji a kan babban titin Kano zuwa Gwarzo. Mashawarcin gwamnan Kano ya ce za a mayar da Kurmawa gidan tarihi ne domin taskance abub...