Sunday, April 26
Shadow
Kwanannan Gwamnatin Tinubu zata koma neman bashi a wajan Opay>>Inji Sanata Dino Melaye

Kwanannan Gwamnatin Tinubu zata koma neman bashi a wajan Opay>>Inji Sanata Dino Melaye

Duk Labarai
Sanata Dino Melaye ya bayyana cewa, akwai yiyuwar Gwamnatin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ta koma neman bashi a wajan Opay. Gwamnatin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu na shan suka saboda yawan cin bashi. Kwanannan ADC ta soki shugaban kasar da cewa, bashin da ake bin Najeriya zai iya kaiwa Naira Tiriliyan 200 nan da watan Disamba. Sakataren yada labarai na ADC, Mallam Bolaji Abdullahi ya bayyana cewa bashin da shugaba Tinubu ya ciyo yafi wanda shugaba Buhari yaci. A hirar da aka yi dashi a Arise TV, Sanata Dino Melaye ya bayyana cewa, Gwamnatin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ta jefa dubban 'yan Najeriya cikin yunwa duk da yawan bashin da take ciyowa. Malaye yace be san dalilin da yasa shugaban ke ciwo bashin makudan kudade ba sannan bai san me yasa 'yan majalisa ke ami...
Ba zaki dawo majalisa ba>>’Yan majalisar suka sanar da Sanata Natasha Akpoti

Ba zaki dawo majalisa ba>>’Yan majalisar suka sanar da Sanata Natasha Akpoti

Duk Labarai
Hukumar kula da majalisar tarayya ta ki amincewa da komawar sanata Natasha Akpoti majalisar bayan data kammala dakatarwar watanni 6 da aka mata. Hukumar tace har yanzu dakatarwar da akawa Sanata Natasha na aiki har sai bayan samun hukuncin kotun daukaka kara. A baya dai sanata Natasha Akpoti ta kai majalisar kotun tarayya amma majalisar ta yi nasara akanta wanda daga baya ta daukaka kara. Har yanzu dai maganar na gaban kotun daukaka kara wanda majalisar tace ba zata iya daukar wani mataki akan lamarin ba sai bayan hukuncin kotu.
Kuma Dai: Bayan X, Hukumar DSS ta kuma aikawa Facebook bukatar kulle shafin Sowore

Kuma Dai: Bayan X, Hukumar DSS ta kuma aikawa Facebook bukatar kulle shafin Sowore

Duk Labarai
Hukumar 'yansandan farin kaya, DSS ta aikawa da kamfanin Meta me mallakar Facebook da bukatar kulle shafin mawallafin jaridar Sahara Reporters kuma me ikirarin kare hakkin bil'adama, Omoyele Sowore. DSS kamar yanda suka aikawa X sun bukaci cewa, Facebook su kulle shafin Sowore saboda sakon da ya wallafa me cewa shugaban kasa me laifine sannan kuma ya yi karya a Brazil inda yace ya magance matsalar rashawa da cin hanci amma a zahiri bai magance din ba. DSS kamar yanda suka gayawa X sun ce wannan sakon ya kawo matsalar tsaro da cin zarafi ga shugaban kasa da sauransu. Saidai Sowore duk da wannan bai nuna alamar nadama ba.
Ji irin Wilakancin da Inyamuray sukawa El-Rufai a Jihar Imo, sun ce yanda bayya sonsu suma basa sonsa

Ji irin Wilakancin da Inyamuray sukawa El-Rufai a Jihar Imo, sun ce yanda bayya sonsu suma basa sonsa

Duk Labarai
Tsohon Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya kai ziyara jihar Imo tare sa Tsohon dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour party a zaben shekarar 2023, Watau Peter Obi. Sun je halartar wani taron bita da aka shirya ne a birnin Owerri na jihar ta Imo ranar Asabar. Saidai sun fuskanci zanga-zanga inda iyamurai da yawa suka taru suka ce El-Rufai ba zai shiga dakin taron ba saboda irin abinda yawa Kiristoci a lokacin da yayi gwamnan jihar Kaduna. Sun kuma ce Peter Obi ya ci amanarsu kuma sun daina goyon bayansa tunda ya kawo musu makiyinsu jiharsu. Rahoton yace masu zanga-zangar inyamurai sun rika daga kwalaye masu dauke da rubutun cewa kai ma Peter Obi ka zama makiyin mu kuma mutuncinka ya zube a idonmu saboda kawo mana El-Rufai. Rahoton yace jami'an tsaro s...
Kalli Bidiyon: Wannan shekarar mun yi Maulidi me tsafta, Ba’a ce an rika ganin Shehu a Sama ko a jikin gini ba, ganin cewa kawai muka rika yi yana wucewa ta gaban mu>>Inji Anisee

Kalli Bidiyon: Wannan shekarar mun yi Maulidi me tsafta, Ba’a ce an rika ganin Shehu a Sama ko a jikin gini ba, ganin cewa kawai muka rika yi yana wucewa ta gaban mu>>Inji Anisee

Duk Labarai
Shahararren dan Darika, Alhaji Anisee Ya bayyana cewa a bana sun yi Maulidi me tsafta. Ya bayyana cewa basu rika ganin Shehu a Gajimare ba ko kuma a jikin gine-gineba, Yace a wannan shekarar sun rika ganin Shehu ne a zahiri yana wucewa ta gabansu. https://www.tiktok.com/@alhajianisee1/video/7547230384145173768?_t=ZS-8zYJAL0uyAL&_r=1
Kalli Bidiyon: Yanda Farfesa Sheikh Isa Ali Pantami ya fashe da kuka saboda takaicin masu son raba kan Hausawa da Fulani

Kalli Bidiyon: Yanda Farfesa Sheikh Isa Ali Pantami ya fashe da kuka saboda takaicin masu son raba kan Hausawa da Fulani

Duk Labarai
Malamin Addinin Islama, Sheikh Isa Ali Pantami ya nuna damuwa matuka akan masu son kawo rabuwar kai tsakanin Hausawa da Fulani. A wani wa'azinsa, An ga Malam ya fashe da kuka inda yace yanzu har akwai wanda zai kawo mana kabilanci kuma har a yadda dashi? https://www.tiktok.com/@professorisaalipantami/video/7545900646709595410?_t=ZS-8zYC14zKUIz&_r=1
Kalli Bidiyo: Yanda wasu musulmai a kasar Amurka suka fito suna neman a Haramta Shan giya, Cin Nqmqn Alade da Caca

Kalli Bidiyo: Yanda wasu musulmai a kasar Amurka suka fito suna neman a Haramta Shan giya, Cin Nqmqn Alade da Caca

Duk Labarai
Wannan wasu musulmai ne a kasar Amurka da suka fito suke zanga-zanga dan neman a haramta cin naman Alade da shan giya da caca Lamarin ya farune a Texas inda abin ya matukar dauki hankula sosai wasu na cewa suna da 'yancin yin hakan wasu kuma na ganin yin hakan ganganci ne. Kalli Bidiyonsu a kasa: https://twitter.com/RadioGenoa/status/1964713441899565330?t=xzY6NH0Q3Rz5MgL3aZbY4A&s=19
Kalli Bidiyon: Ana ta cece-kuce, ‘Yan Najeriya na mamaki bayan ganin katafaren gidan tsohon Gwamnan Abia, Orji Kalu a kasar Amurka

Kalli Bidiyon: Ana ta cece-kuce, ‘Yan Najeriya na mamaki bayan ganin katafaren gidan tsohon Gwamnan Abia, Orji Kalu a kasar Amurka

Duk Labarai
An ga katafaren gida na Alfarma da tsohon gwamnan jihar Abia, Orji Kalu ya mallaka a Maryland dake kasar Amurka. Lamarin ya dauki hankula sosai inda akai ta cece-kuce wasu na fadin cewa abin birgewane inda wasu kuma ke cewa ba da kudinsa ya saya ba. https://twitter.com/ChuksEricE/status/1964690041445503097?t=QNJuC22yYEtxJ5F_MOYxzQ&s=19
Baiwa jami’an mu kudi, cin hanci laifi ne, ku daina dauke musu hankali daga gudanar da aiki yanda ya kamata>>Hukumar ‘Yansandan Najeriya ta gargadi mutane

Baiwa jami’an mu kudi, cin hanci laifi ne, ku daina dauke musu hankali daga gudanar da aiki yanda ya kamata>>Hukumar ‘Yansandan Najeriya ta gargadi mutane

Duk Labarai
Hukumar 'yansandan Najeriya ta garagadi Mutane da cewa, baiwa 'yansandan Najeriya kudi ko cin hanci a yayin da suke bakin aiki shima laifi ne. Hukumar ta gargadi 'yan Najeriya da su yi hankali su daina daukewa 'yansandan hankali daga aikin da suke. Sanarwar ta fito ne daga bakin hukumar 'yansandan babban birnin tarayya Abuja. https://twitter.com/FCT_PoliceNG/status/1964752773083181153?t=Hw13v97hldjZVynO-RQ3Lg&s=19