Monday, December 22
Shadow
Ana tsaka da min Tiyata a Asibiti, sai na ji na Mutu, kuma na hadu da Jesus har ya nuna min Aljannah>>Inji Wannan Mutumin

Ana tsaka da min Tiyata a Asibiti, sai na ji na Mutu, kuma na hadu da Jesus har ya nuna min Aljannah>>Inji Wannan Mutumin

Duk Labarai
Wani mutum da yayi ikirarin ya mutu a yayin da ake tsaka da yi masa tiyata ya bayyana cewa ya hadu da Annabi Isa(AS) watau Jesus kuma wai har ya nuna masa Aljannah. Mutumin me suna Mike McKinsey dake California ta kasar Amurka ya bayyana cewa, yayi mutuwar ne ta mintuna 45. Likitoci sun bayyana cewa aikinsa ne mafi mamaki da hadari da suka taba yi inda suka ce wai ya mutu na dan wani lokaci a yayin da suke masa aikin cire appendix. Sun ce zuciyar mutumin ta daina bugawa sannan ya daina numfashi amma sun yi nasarar dawo dashi. Yace da ya mutun, ya ga Jesus wanda yayi kama da Balarabe. Yace Jesus din ya bashi hannu ya daukeshi zuwa wani guri me kyau da bai taba gani ba. Yace anan ne yasan cewa ba zai mutu ba. Ya kara da cewa, sai kawai ya farfado inda ya tabbatar cewa l...
Wata Sabuwa: Kasar Amurka ta ce bata amince da tsayar da Kìsàn Falasdiynawa ba a Gàzà

Wata Sabuwa: Kasar Amurka ta ce bata amince da tsayar da Kìsàn Falasdiynawa ba a Gàzà

Duk Labarai
Amurka ta hau kujerar na-ƙi game ƙudirin da aka gabatar a Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya na tsagaita wuta a yaƙin Gaza ta dindindin ba tare da sharaɗi ba. Sauran mambobin kwamitin 14 sun amince da buƙatar ƙudirin, wanda kuma ya buƙaci sakin duka Isra'ilawa da ake garkuwa da su tare da ɗage taƙaita shigar da agaji zuwa Gaza. Jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniyar, Dorothy Camille Shea, ta ce ƙudirin ya gaza shafar kowane ɓangare saboda bai yi kira ga Hamas ta ajiye makamanta tare da ficewa daga Zirin Gaza ba.
Kifewar kwale-kwale ta kàshe mutum biyar a jihar Sokoto

Kifewar kwale-kwale ta kàshe mutum biyar a jihar Sokoto

Duk Labarai
Mutum bakwai ne suka rasu sakamakon kifewar kwalekwale a yankin ƙaramar hukumar Shagari da ke jihar Sokoto a arewacin Najeriya. Lamarin ya faru ne a lokacin da matafiyan suka fito daga Gidan Hussaini zuwa ƙauyen Gwargawu a ranar Litinin da misalin ƙarfe 9:30 na safiya, kamar yadda hukumar bayar da agaji ta ƙasa Nema ta bayyana. Nema ta ce bayanai sun nuna iska mai ƙarfi ce ta haddasa kifewar jirgin ruwan. A watan Oktoban 2024 ma wani jirgi ya kife da kusan mutum 300 a yankin Mokwa na jihar Neja da ke tsakiyar Najeriyar. Kafin haka, mutum 24 ne suka mutu a kifewar wani jirgin a watan Satumban 2023 a jihar.
Tinubu ya bai wa mutanen Mokwa tallafin naira biliyan biyu da shinkafa tirela 20

Tinubu ya bai wa mutanen Mokwa tallafin naira biliyan biyu da shinkafa tirela 20

Duk Labarai
Mataimakin shugaban Najeriya, Kashim Shettima ya ce shugaban ƙasar Bola Tinubu ya amince da bai wa mutanen da ambaliyar ruwa ta shafa a jihar Neja gudumawar kuɗi naira biliyan biyu da kuma tirela 20 na shinkafa. Shettima ya sanar da hakan ne a garin Mokwa, lokacin ziyarar da ya kai bayan ambaliyar ruwa da ta ɗaiɗaita garin wadda ta lalata dukiya da kadarori da kuma sanadiyyar salwantar ɗaruruwan rayuka. Mataimakin shugaban ƙasar ya ce za a magance duk wasu matsaloli da ke addabar al'ummar. Inda ya ce shugaban ƙasar ya bayar da umarnin gyara gadojin da ambaliyar ta lalata ba tare da ɓata lokaci ba. Hukumomi sun tabbatar da mutuwar sama da mutum 200 a ambaliyar ta ƙaramar hukumar Makwa da ke jihar Neja a arewa ta tsakiyar Najeriya. Haka nan akwai sama da mutum 500 da ba a san ...
Gwamna Adeleke na Osun ya gana da Tinubu a Legas

Gwamna Adeleke na Osun ya gana da Tinubu a Legas

Duk Labarai
Gwamnan jihar Osun Ademola Adeleke ya kai ziyara ga shugaban Najeriya, Bola Tinubu a gidanke da ke birnin Legas. Cikin wani saƙo da gwamnan ya wallafa a shafinsa na X, ya ce ya kai ziyarar ne tare da ƴan'uwansa, babban yayaransa Adedeji Adeleke, da kuma ɗandan'uwansa, fitaccen mawaƙin nan David Adeleke da aka fi sani da Davido, gabanin bukukuwan babbar sallah. Kodayake babu cikakken bayani kan abin da tattaunawar tasu ta ƙunsa, ganawar na zuwa ne kwanaki bayan Davido ya gana da Tinubu a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja, a wani abu da ake ganin tattaunawa ce tsakanin dangin Adeleke da fadar shugaban ƙasar. A cikin watan da ya gabata ne hukumar zaɓen Najeriya, INEC ta saka ranar 20 ga watan Yulin 2026 a matsayin ranar da za ta gudanar da zaɓen gwamnan jihar Osun. Ana ganin Gwamna ...
Ban taɓa zuwa wurin boka don neman sa’a ba>>Inji Gwamnan Jihar Anambra, Charles Soludo

Ban taɓa zuwa wurin boka don neman sa’a ba>>Inji Gwamnan Jihar Anambra, Charles Soludo

Duk Labarai
Gwamnan jihar Anambra, Farfesa Chukwuma Soludo ya yi watsi da raɗe-raɗin da ake yaɗawa cewa ya tuntuɓi wani boka domin buƙatar sake zaɓarsa matsayin gwamnan jihar a wa'adi na biyu. Ranar 8 ga watan Nuwamban shekarar da muke ciki ne hukumar zaɓen Najeriya ta saka domin gudanar da zaɓen gwamnan jihar. A cinin ƴan kwanakin nan ne wani bidiyo ya karaɗe shafukan sada zumunta da ke iƙirrarin cewa gwamnan ya tuntuɓi wani boka domin neman ''sa'ar'' sake zaɓarsa. To sai dai cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labaran gwamnan, Christian Aburime, ya fitar, gwamnan ya bayayna zargin a matsayin ''tsagwaron ƙarya''. Sanarwar ta ce bidiyon da ake yaɗawar an ɗauke shi ne a lokacin wani taro da jami'an gwamnati suka yi da masu wallafa abubuwa a shafukan sada zumunta na jihar.
Matashi Daga Jihar Bauchi Zai Nufi Jihar Lagos Ranar Alhamis Domin Ya Je Ya Gwangwaje Shugaba Tinubu Da Ragon Sallah

Matashi Daga Jihar Bauchi Zai Nufi Jihar Lagos Ranar Alhamis Domin Ya Je Ya Gwangwaje Shugaba Tinubu Da Ragon Sallah

Duk Labarai
Matashi Daga Jihar Bauchi Zai Nufi Jihar Lagos Ranar Alhamis Domin Ya Je Ya Gwangwaje Shugaba Tinubu Da Ragon Sallah. {"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Khamis Musa Darazo, wani mai kaunar shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu daga jihar Bauchi, ya shirya kai ragon Sallah zuwa Lagos domin gabatar da kyautar godiya ga shugaban kasa saboda amincewarsa da lasisin hakar mai na Kolmani. Khamis ya shaidawa jaridar Vanguard a ranar Litinin cewa, bayan ya tattauna da dattawan yankinsa, ya yanke shawarar daukar ragon zuwa jihar ...
Gwamnatin jihar Neja ta soke hawan sallah sakamakon ambaliyyar ruwa a Mokwa

Gwamnatin jihar Neja ta soke hawan sallah sakamakon ambaliyyar ruwa a Mokwa

Duk Labarai
Gwamnatin jihar Neja ta soke hawan sallah sakamakon ambaliyyar ruwa a Mokwa. Gwamnan jihar Neja, Umaru Bago, ya bada umarnin soke bukukuwan babbar sallah tare da dakatar da Hawan Bariki, da sauran bukukuwan Sallah a dukkan masarautun jihar. Umurnin ya biyo bayan mummunan ibtila'in ambaliyar ruwa da ta yi sanadin asarar rayuka da dukiyoyi a garin Mokwa da kewaye. Sakataren gwamnatin jihar, Alhaji Abubakar Usman a lokacin da ya ke sanar da wannan umarni, ya ce an dauki matakin ne a matsayin girmamawa ga wadanda lamarin ya rutsa da su da kuma ba da damar zaman makoki da addu’o'i. Da ya ke mika umarnin Gwamnan ga Masarautu, Sakataren Gwamnatin ya bayyana cewa, ambaliyar Mokwa na daya daga cikin mafi muni da aka yi a jihar tsawon shekaru da dama da suka gabata, kuma ya yi sanadi...
Hajjin bana: Saudiyya ta hana ɗaukar hoto da taron siyasa a guraren ibada

Hajjin bana: Saudiyya ta hana ɗaukar hoto da taron siyasa a guraren ibada

Duk Labarai
Hukumomin Saudiyya sun hana daukar hoto, taruka da harkokin siyasa da daga tutoci a wuraren ibada yayin aikin Hajjin bana na 2025. A wata sanarwa da ma’aikatar harkokin cikin gida ta kasar ta fitar, masarautar ta bayyana cewa mahajjata ba su da izinin daukar hoto ko yin bidiyo a Masallacin Harami da ke Makkah, da Masallacin Annabi da ke Madinah, da kuma muhimman wuraren aikin hajji irin su Mina, Arafat da Muzdalifah. Ma’aikatar ta ce wannann umarni ya shafi wayoyin hannu da kuma na’urorin daukar hoto na kwararru, tare da gargadin kada a daga tuta ko alluna da ke dauke da alamomin siyasa, kabila ko akida. Hukumomin sun sake jaddada cewa irin wadannan ayyuka na iya lalata yanayin ibada da kuma haifar da rarrabuwar kai tsakanin mahajjata.